Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 19

Ayyukan Manzanni 19:9-28

Help us?
Click on verse(s) to share them!
9Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus.
10Haka ya cigaba shekaru biyu har duk mazaunan Asiya suka ji maganar Ubangiji, Yahudawa da Helenawa.
11Allah ya yi manyan al'ajibai ta hannun Bulus,
12har marasa lafiya suka warke, mugayen ruhohi suka fito daga cikin mutane, sa'adda suka karbi kyallaye da mayafai daga jikin Bulus.
13Amma akwai Yahudawa masu tsubu da suka biyo ta wajen, suka dauka wa kansu su yi amfani da sunan Yesu. Suka ce, “Mun dokace ku cikin sunan Yesu wanda Bulus yake wa'azinsa, ku fita.”
14Wadanda suka yi wannan su bakwai ne 'ya'yan wani babban firist Bayahude mai suna Siba.
15Mugun ruhun ya amsa ya ce, “Na san Yesu, na san Bulus, amma ku, su wanene?”
16Sai mugun ruhun da ke cikin mutumin ya fada a kan matsubatan ya fi karfinsu ya kuma bubuge su. Suka runtuma da gudu suka fice daga dakin tsirara da raunuka.
17Wannan ya zama sanannen abu ga dukan mutane, Yahudawa da Helenawa mazaunan Afisa. Suka ji tsoro kwarai, sunan Ubangiji Yesu ya sami daukaka.
18Masu bi da yawa kuma, suka zo suka furta mugayen ayyukan da suka aikata.
19Masu sihiri suka kawo littattafansu suka kona a gaban mutane. Da aka yi jimilar tamaninsu, aka samu sun kai dubu hamsin na azurfa.
20Sai maganar Ubangiji ta yadu da iko ta hanyoyi da yawa.
21Da Bulus ya kammala aikinsa na bishara a Afisa, Ruhu ya bishe shi sai ya bi ta Makidoniya da Akiya a kan hanyarsa zuwa Urushalima. Ya ce, “Bayan na je can, dole in je Roma.”
22Bulus ya aiki almajiransa biyu Timoti da Irastus zuwa Makidoniya, wadanda suka taimake shi. Amma shi da kansa ya jira a Asiya na dan lokaci.
23A wannan lokacin sai aka yi babban tashin hankali a Afisa game da wannan Hanyar.
24Wani Makeri mai suna Damatrayus wanda ke kera sifoffin gunkin azurfa na Dayana, wanda sana'a ce mai kawo wa makera riba sosai.
25Ya tattara makera ya ce da su, “Kun sa ni da wanan sana'a ne muke samun kudi mai yawa.
26Kun gani kun kuma ji cewa, ba a Afisa kadai ba, amma har da fadin kasar Asiya wannan Bulus ya rinjayi mutane da yawa. Yana cewa babu alloli da ake kerawa da hannu.
27Ba sana'ar mu kadai ke cikin hatsari ba, amma har da haikalin allahnmu Dayana babba zai zama mara amfani. Ta haka za ta rasa girmanta, ita da dukan kasar Asiya da duniya ke wa sujada.”
28Da suka ji haka sai suka fusata kwarai, suka yi kira mai karfi suna cewa “Mai girma ce Dayana ta Afisa.”

Read Ayyukan Manzanni 19Ayyukan Manzanni 19
Compare Ayyukan Manzanni 19:9-28Ayyukan Manzanni 19:9-28