Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 19:1-9 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 19:1-9 in Litafi Mai-tsarki

1 Sa'adda Afolos yake a Koranti, Bulus ya zagaya kasar tudu ya zo birnin Afisa, a nan kuma ya sami wadansu almajirai.
2 Bulus ya ce masu, “Ko kun karbi Ruhu Mai Tsarki sa'anda kuka ba da gaskiya?” Suka amsa, “A'a bamu taba jin labarin Ruhu Mai Tsarki ba.
3 Bulus ya ce, “Wacce irin baftisma aka yi maku?” Suka ce, “Baftismar Yahaya”
4 Bulus ya amsa ya ce, “Yahaya ya yi wa mutane baftismar tuba, ya ce su ba da gaskiya wanda zai zo bayansa, wato, Yesu kenan.”
5 Da mutanen suka ji haka, sai aka yi masu baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu.
6 Sa'adda Bulus ya dibiya hannu a kansu, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauka a kansu suka yi magana da harsuna da kuma annabci.
7 Su wajen mutum goma sha biyu ne.
8 Bulus ya shiga majami'a ya yi ta koyarwa gabagadi misalin tsawon wata uku. Yana bi da su cikin nazarin maganar yana fahimtar da mutane su gaskanta game da abubuwa da suka shafi mulkin Allah.
9 Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus.
Ayyukan Manzanni 19 in Litafi Mai-tsarki