Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 19

Ayyukan Manzanni 19:1-9

Help us?
Click on verse(s) to share them!
1Sa'adda Afolos yake a Koranti, Bulus ya zagaya kasar tudu ya zo birnin Afisa, a nan kuma ya sami wadansu almajirai.
2Bulus ya ce masu, “Ko kun karbi Ruhu Mai Tsarki sa'anda kuka ba da gaskiya?” Suka amsa, “A'a bamu taba jin labarin Ruhu Mai Tsarki ba.
3Bulus ya ce, “Wacce irin baftisma aka yi maku?” Suka ce, “Baftismar Yahaya”
4Bulus ya amsa ya ce, “Yahaya ya yi wa mutane baftismar tuba, ya ce su ba da gaskiya wanda zai zo bayansa, wato, Yesu kenan.”
5Da mutanen suka ji haka, sai aka yi masu baftisma cikin sunan Ubangiji Yesu.
6Sa'adda Bulus ya dibiya hannu a kansu, Ruhu Mai Tsarki kuma ya sauka a kansu suka yi magana da harsuna da kuma annabci.
7Su wajen mutum goma sha biyu ne.
8Bulus ya shiga majami'a ya yi ta koyarwa gabagadi misalin tsawon wata uku. Yana bi da su cikin nazarin maganar yana fahimtar da mutane su gaskanta game da abubuwa da suka shafi mulkin Allah.
9Amma sa'adda wadansu Yahudawa suka taurare, suka ki yin biyayya, sai suka fara bata hanyar Almasihu a gaban taron. Saboda haka sai Bulus ya janye daga wurinsu tare da wadanda suka ba da gaskiya. Ya fara koyarwa a makarantar Tiranus.

Read Ayyukan Manzanni 19Ayyukan Manzanni 19
Compare Ayyukan Manzanni 19:1-9Ayyukan Manzanni 19:1-9