Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 15:16-20 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 15:16-20 in Litafi Mai-tsarki

16 'Bayan wadannan abubuwa zan dawo, zan gina gidan Dauda wanda ya fadi kasa; in sake gina bangonsa, in tsayar da shi,
17 saboda sauran jama'a su nemi fuskar Ubangiji, har da al'ummai da ake kira da sunana.
18 Wannan shine abin da Ubangiji ya fadi, shi wanda ya yi wadannan abubuwa da aka sani tun zamanin da.
19 Saboda haka, a gani na kada mu matsa wa al'umman da suka juyo gun Allah;
20 amma zamu rubuta masu da cewa, su guje wa gumaka da zina da faskanci da maye da cin mushe.
Ayyukan Manzanni 15 in Litafi Mai-tsarki