Text copied!
Bibles in Hausa

Ayyukan Manzanni 14:18-28 in Hausa

Help us?

Ayyukan Manzanni 14:18-28 in Litafi Mai-tsarki

18 Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya.
19 Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu.
20 Duk da haka da almajirai suka kewaye shi a tsaitsaye, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari, ya tafi Darba tare Barnaba.
21 Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya.
22 Suna karfafa zuciyar almajiran su rike bangaskiyarsu, su ci gaba da ita, suna ce masu, “Ta wurin jimrewa mai yawa zamu shiga mulkin Allah, don haka dole ne mu sha wahala.”
23 Da suka zabar masu dattawa a kowace iklisiya, sai suka yi addu'oi da azumi, suka mika su ga Ubangiji, ga wanda suka gaskanta a gareshi.
24 Sa'annan sun bi ta Bisidiya suka kai Bamfiliya.
25 Da suka yi maganarsu a Biriya, sun wuce zuwa har Italiya.
26 Ta jirgin ruwa zuwa Antakiya, a nan ne aka mika su ga alherin Allah don aikin da suka gama a yanzu.
27 Da isowarsu Antakiya sun tara 'yan iklisiya a wuri daya, sun ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda Ya bude kofa a wurin al'ummai ta bangaskiya.
28 Sun zauna tare da almajiran na tsawon lokaci.
Ayyukan Manzanni 14 in Litafi Mai-tsarki