Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 14

Ayyukan Manzanni 14:18-28

Help us?
Click on verse(s) to share them!
18Duk da wadannan kalmomin da kyar, Bulus da Barnaba suka iya tsayar da su daga yi masu hadaya.
19Amma wasu Yahudawa daga Antakiya da wasunsu daga Ikoniya suka rinjayi tarun jama'ar. Suka jajjefi Bulus suka ja shi zuwa wajen garin, suna ganin kamar ya mutu.
20Duk da haka da almajirai suka kewaye shi a tsaitsaye, sai ya tashi ya koma cikin garin. Washegari, ya tafi Darba tare Barnaba.
21Bayan sun yi wa'azin bishara a wannan birnin suka kuma sami almajirai da yawa, suka dawo Listira, da Ikoniya da Antikiya.
22Suna karfafa zuciyar almajiran su rike bangaskiyarsu, su ci gaba da ita, suna ce masu, “Ta wurin jimrewa mai yawa zamu shiga mulkin Allah, don haka dole ne mu sha wahala.”
23Da suka zabar masu dattawa a kowace iklisiya, sai suka yi addu'oi da azumi, suka mika su ga Ubangiji, ga wanda suka gaskanta a gareshi.
24Sa'annan sun bi ta Bisidiya suka kai Bamfiliya.
25Da suka yi maganarsu a Biriya, sun wuce zuwa har Italiya.
26Ta jirgin ruwa zuwa Antakiya, a nan ne aka mika su ga alherin Allah don aikin da suka gama a yanzu.
27Da isowarsu Antakiya sun tara 'yan iklisiya a wuri daya, sun ba da labarin dukan abin da Allah ya yi ta wurinsu. Da yadda Ya bude kofa a wurin al'ummai ta bangaskiya.
28Sun zauna tare da almajiran na tsawon lokaci.

Read Ayyukan Manzanni 14Ayyukan Manzanni 14
Compare Ayyukan Manzanni 14:18-28Ayyukan Manzanni 14:18-28