Text copied!
CopyCompare
Litafi Mai-tsarki - Ayyukan Manzanni - Ayyukan Manzanni 11

Ayyukan Manzanni 11:17-21

Help us?
Click on verse(s) to share them!
17To, idan Allah ya yi masu baiwa kamar yadda ya yi mana yayin da muka bada gaskiya ga Ubangiji Yesu Almasihu, wane ni da zan yi jayayya da Allah?
18Da suka ji wadannan abubuwa, suka rasa ta cewa, amma suka daukaka Allah suka ce “Ga al'ummai ma Allah ya basu tuba zuwa rai.”
19Sai wadanda suka warwatsu saboda tsananin da ya bi bayan mutuwan Istifanas, suka yadu har zuwa Finikiya, Kuburus da Antakiya, amma suka yi wa'azin Yesu ga Yahudawa kadai.
20Amma wadan sunsu, mutane daga Kuburus da Kurane, suka zo Antakiya suka yi magana da hellenawa, suna yi masu wa'azin Ubangiji Yesu.
21Kuma ikon Ubangiji yana tare da su, har mutane da yawa suka gaskata kuma suka juyo wurin Ubangiji.

Read Ayyukan Manzanni 11Ayyukan Manzanni 11
Compare Ayyukan Manzanni 11:17-21Ayyukan Manzanni 11:17-21