Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 9:22-33 in Hausa

Help us?

Yahaya 9:22-33 in Litafi Mai-tsarki

22 Iyayensa sun fadi wadannan abubuwan, domin suna ji tsoron Yahudawan. Gama Yahudiyawan sun rigaya sun yarda duk wanda yace Yesu Almasihu ne, za a fitar dashi daga majami'a.
23 Domin wannan ne, iyayensa suka ce, “Ai shi ba yaro ba ne, ku tambaye shi.”
24 Suka sake kiran mutumin dake makaho karo na biyu, suka ce masa, “Ka girmama Allah. Mu kam mun sani wannan mutum mai zunubi ne.”
25 Sai wannan mutum ya amsa, “Ban sani ba ko shi mai zunubi ne. Abu guda daya na sani: da Ni makaho ne, amma yanzu ina gani.”
26 Sai su ka ce masa, “Me ya yi maka? Ta yaya ya bude idanunka?”
27 Ya amsa, “Na rigaya na gaya maku, amma ba ku ji ba! Don me kuke so ku sake ji? Ko kuma kuna so ku zama almajiransa, haka ne?
28 Sai suka kwabe shi suka ce, “kai ne almajirinsa, amma mu almajiran Musa ne.
29 Mun sani Allah ya yi magana da Musa, amma wannan mutum, bamu san ko daga ina ne ya zo ba.”
30 Mutumin ya amsa masu ya ce, “Tirkashi, baku san inda ya fito ba, duk da haka shi ya bude mani idanu.
31 Mun san da cewa Allah baya jin masu zunubi, amma idan wani mai ibada ne yana kuma yin nufinsa, to yana jin sa.
32 Tunda duniya ta fara ba a taba jin cewa wani ya bude idanun wanda aka haifa makaho ba.
33 In mutumin nan ba daga Allah yake ba, ba zai iya yin komai ba.”
Yahaya 9 in Litafi Mai-tsarki