Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 9:1-5 in Hausa

Help us?

Yahaya 9:1-5 in Litafi Mai-tsarki

1 Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa.
2 Sai almajiransa suka tambaye shi, “Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?”
3 Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa.
4 Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki.
5 Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya.”
Yahaya 9 in Litafi Mai-tsarki