Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 9:1-18 in Hausa

Help us?

Yahaya 9:1-18 in Litafi Mai-tsarki

1 Da Yesu yana wucewa, sai ya ga wani mutum makaho tun daga haihuwa.
2 Sai almajiransa suka tambaye shi, “Mallam, wa yayi zunubi, mutumin ne ko iyayensa, har aka haife shi makaho?”
3 Yesu ya amsa, Ba mutumin ne ko iyayensa suka yi zunubi ba, amma domin aikin Allah ya bayyana a cikinsa.
4 Dole mu yi aikin wanda ya aiko ni tunda rana. Dare na zuwa inda ba mai iya yin aiki.
5 Yayinda ina duniya, ni ne hasken duniya.”
6 Bayan da Yesu ya fadi wadannan abubuwan, ya tofa yawu a kasa, ya kwaba kasar da yawunsa, sai ya shafe idanun mutumin da kasar.
7 Ya ce masa, tafi, ka wanke a tafkin Siloam (ma'anarsa: aike).” Sai mutumin ya tafi, ya wanke, ya dawo yana gani.
8 Sai makwabtansa da mutanen da da suka gan shi tun can yana roko suka ce, “Ba wannan mutum ne wanda ya ke zaune yana roko ba?”
9 Wadansu suka ce, “shi ne.” Wadansu suka ce, “A'a, amma yana kama da shi.” Amma shi ya ce, “Ni ne wannan mutum.”
10 Suka ce masa, “To yaya aka bude maka idanu?”
11 Sai ya amsa, “Mutumin da ake ce da shi Yesu shi ya kwaba kasa ya shafa mani a idanuna ya ce mani, 'je ka kogin Siluwam ka wanke.' Sai naje na wanke, sannan na samu gani.”
12 Suka ce masa, “Ina yake?” Ya amsa, “Ban sani ba.”
13 Suka kawo mutumnin da yake makaho a da wurin farisawa.
14 A ranar asabar ne kwa Yesu ya kwaba kasa ya bude masa idanu.
15 Har yanzu farisawan suka tambaye shi yadda ya sami ganin gari. Ya ce masu, “Ya sa mani kasa a idanuna, na wanke, kuma yanzu ina gani.”
16 Wadansu daga cikin farisawa suka ce, “Wannan mutum ba daga Allah yake ba domin ba ya kiyaye ranar Asabar. “Wadansu suka ce, “Yaya mai zunubi zai yi irin wadannan alamu?” Sai rabuwa ta shiga tsakanin su.
17 Sai suka tambayi makahon kuma, “Me kake cewa game da shi dashike ya bude maka idanu?” Makahon ya ce, “shi annabi ne.”
18 Har yanzu kam Yahudawan basu yarda da makantarsa ba da ganin gari da ya samu, sai da suka kirayo iyayen shi wanda ya sami ganin garin.
Yahaya 9 in Litafi Mai-tsarki