Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 8:6-17 in Hausa

Help us?

Yahaya 8:6-17 in Litafi Mai-tsarki

6 Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa.
7 Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, “shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse.”
8 Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa.
9 Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su.
10 Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, “mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki?
11 Ta ce, “Ba kowa, Ubangiji” Yesu ya ce, “Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi.”
12 Yesu ya kara yin magana da mutanen cewa, “Ni ne hasken duniya, shi wanda ya biyo ni, ba zai yi tafiya cikin duhu ba, amma za ya sami hasken rai.
13 Farisawa suka ce masa, “Kana bada shaida a kan ka, shaidarka ba gaskiya ba ce.”
14 Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
15 Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
16 Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
17 I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
Yahaya 8 in Litafi Mai-tsarki