Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 8:31-59 in Hausa

Help us?

Yahaya 8:31-59 in Litafi Mai-tsarki

31 Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, “Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya,
32 Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku.”
33 Suka amsa masa, “Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?”
34 Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, dukan wanda ya ke aika zunubi bawan zunubi ne.
35 Bawa kuwa, ba ya zama a gida dindindin, da yana zama dindindin.
36 Saboda haka, idan Dan ya 'yantar da ku zaku zama 'yantattu sosai.
37 Na san ku zuriyar Ibrahim ne, kuna so ku kashe ni saboda kalma ta bata da wurin zama a cikin ku.
38 Na fadi abubuwan da na gani a wurin Ubana, ku kuma kuna yin abubuwan da kuka ji daga wurin ubanku.”
39 Suka amsa suka ce masa, “Ibrahim ne ubanmu” Yesu ya ce masu, “Da ku 'yayan Ibrahim ne da kun yi ayukan da Ibrahim ya yi.
40 Amma, yanzu kuna so ku kashe ni, mutumin da ya gaya maku gaskiyar da ya ji daga wurin Allah. Ibrahim bai yi haka ba.
41 Kuna yin ayyukan ubanku. Suka ce masa, “mu ba a haife mu cikin fasikanci ba, muna da Uba daya: Allah.”
42 Yesu ya ce masu, “Inda Allah Ubanku ne, da kun kaunace ni, gama na zo daga wurin Allah kuma ga ni anan, gama ba domin kaina nazo ba, shine ya aiko ni.
43 Meyasa baku gane magana ta ba? Ai saboda ba za ku iya jin maganata ba ne.
44 Ku na ubanku, shaidan ne, kuma kuna so ku yi nufe-nufe na ubanku. Shi mai kisan kai ne tun daga farko kuma ba ya tsayawa gaskiya saboda da babu gaskiya a cikin sa. Sa'anda yake fadin karya, yana maganar halinsa ne domin shi dama makaryaci ne da uban karya kuma.
45 Dayake ina fadin gaskiya baku bada gaskiya gare ni ba.
46 Wanene a cikin ku ya kama ni da zunubi? Idan na fadi gaskiya don me ba ku gaskanta ni ba?
47 Shi wanda yake na Allah ya kan ji maganar Allah, ku ba kwa jin maganar Allah da yake ku ba na Allah bane,”
48 Yahudawa suka amsa suka ce masa, “Bamu fadi gaskiya ba da muka ce kai Basamariye ne kuma kana da aljan?”
49 Yesu ya amsa, “Ni ba ni da aljan, ina girmama Ubana, ku kuma ba kwa girmama ni.”
50 Ba na neman daraja domin kaina, akwai wanda ke nema yana kuma hukuntawa.
51 Hakika, hakika, iIna ce maku, dukan wanda ya kiyaye maganata, ba za ya ga mutuwa ba.”
52 Sai Yahudawa su ka ce masa, Yanzu mun sani kana da aljan. Ibrahim da annabawa sun mutu, amma kai ka ce, 'dukan wanda ya yi biyayya da maganata ba zai dandana mutuwa ba'.
53 Ai baka fi ubanmu Ibrahim girma ba wanda ya mutu, ko ka fi shi? Annabawa kuma sun mutu. Wa kake daukar kanka ne?”
54 Yesu ya amsa, “Idan na daukaka kaina, daukaka ta banza ce, Ubana ne ya daukaka ni. Wanda kuka ce shi ne Allahnku.
55 Ku kuwa ba ku san shi ba, amma ni na san shi. Idan na ce ban san shi ba, na zama kamar ku kenan, makaryaci. Sai dai, Ni na san shi ina kiyaye maganarsa.
56 Ubanku Ibrahim ya yi farinciki da ganin rana ta; ya gan ta kuma ya yi murna.”
57 Yahudawa su ka ce masa, “Baka kai shekara hamsin ba tukuna, ka taba ganin Ibrahim?”
58 Yesu ya ce masu, “Hakika, hakika, ina ce maku, kafin a haifi Ibrahim, NI NE.”
59 Suka dauki duwatsu za su jefe shi, amma Yesu ya boye kansa, ya fita daga haikali.
Yahaya 8 in Litafi Mai-tsarki