Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 8:14-33 in Hausa

Help us?

Yahaya 8:14-33 in Litafi Mai-tsarki

14 Yesu ya amsa ya ce masu, “Ko ma na bada shaida a kai na, shaidata gaskiya ce, na san daga inda na fito da inda zan tafi, amma ku baku san daga inda na fito ba, baku kuma san inda zan tafi ba.
15 Kuna shari'a ta son kai, ni ko ban yi wa kowa shari'a ba.
16 Ko ma da na yi shari'a, shari'ata gaskiya ce domin ba ni kadai ba ne, amma ina tare da Uba wanda ya aiko ni.
17 I, a cikin dokarku an rubuta cewa shaidar mutum biyu gaskiya ce.
18 Ni ne ni ke shaidar kaina, kuma Uba wanda ya aiko ni ya na shaida ta.
19 Su ka ce da shi, “Ina ubanka?” Yesu ya amsa ma su ya ce, “baku san ni ba balle Ubana, in da kun san ni da kun san Uba na kuma.”
20 Ya fadi wadannan kalmomi a kusa da wurin ajiya sa'adda ya ke koyarwa a cikin haikali, kuma ba wanda ya kama shi saboda sa'arsa bata yi ba tukuna.
21 Ya kara cewa da su, “Zan tafi, za ku neme ni ba za ku same ni ba, za ku mutu cikin zunubinku. Inda ni ke tafiya, ba za ku iya zuwa ba”.
22 Yahudawa su ka ce, “Zai kashe kansa ne, da ya ce inda ni ke tafiya ba za ku iya zuwa ba?”
23 Yesu ya ce masu ku daga kasa kuke, Ni kuwa daga bisa ni ke. Ku na wannan duniya ne, Ni kuwa ba na wannan duniya ba ne.
24 Shiyasa na ce maku za ku mutu cikin zunubanku. In ba kun bada gaskiya NI NE ba, za ku mutu cikin zunubanku.
25 Sai kuma suka ce da shi, “Wanene kai?” Yesu ya ce masu, “Abin da na gaya maku tun daga farko.
26 Ina da a bubuwa da yawa da zan gaya maku, in kuma hukunta ku a kai. Duk da haka, wanda ya aiko ni, mai gaskiya ne, abubuwan da naji daga wurin sa, wadannan abubuwan su ni ke gaya wa duniya.”
27 Ba su gane ba yana yi masu magana a kan Uban.
28 Yesu ya ce, “Sa'adda kuka tada Dan Mutum sama sa'annan za ku gane NI NE, kuma ban yi komi domin kaina ba. Kamar yadda Uba ya koya mani, haka nike fadin wadannan abubuwa.
29 Shi wanda ya aiko ni, yana tare da ni kuma bai bar ni ni kadai ba, domin kullum ina yin abubuwan da suke faranta masa rai.”
30 Sa'adda Yesu ya ke fadin wadannan abubuwa, dayawa suka bada gaskiya gare shi.
31 Yesu ya gayawa wadancan Yahudawa da suka bada gaskiya gare shi, “Idan kun tsaya a cikin magana ta ku almajiraina ne na gaskiya,
32 Kuma za ku san gaskiya, gaskiya kuwa zata 'yantar da ku.”
33 Suka amsa masa, “Mu zuriyar Ibrahim ne kuma bamu taba yin bauta wurin kowa ba, yaya za ka ce, 'Za a 'yantar da ku'?”
Yahaya 8 in Litafi Mai-tsarki