Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 8:1-11 in Hausa

Help us?

Yahaya 8:1-11 in Litafi Mai-tsarki

1 Yesu ya je Dutsen Zaitun.
2 Da sassafe ya dawo Haikali, dukan mutane kuma suka zo wurin sa; yazauna koya masu.
3 Sai marubuta da Farisawa suka kawo mace wadda aka kama ta tana zina. Su ka sa ta a tsakiya.
4 Sai su ka ce da shi, “Malam, wannan mace an kama ta tana cikin yin zina.
5 A cikin shari'a, Musa ya bamu umurni mu jejjefe irin wandannan mutume, kai me ka ce game da ita?”
6 Sun fadi haka ne domin su gwada shi su sami abinda za su zarge shi da shi, amma Yesu ya sunkuya yayi rubutu da yatsansa a kasa.
7 Sa'adda suka cigaba da tambayar sa, ya mike tsaye yace masu, “shi wanda ba shi da zunubi a cikin ku, ya fara jifar ta da dutse.”
8 Ya sake sunkuyawa, ya yi rubutu da yatsansa a kasa.
9 Da suka ji haka, sai suka fita dai-dai da dai-dai, kama daga babbansu. A karshe dai aka bar Yesu shi kadai, tare da matar wadda ta ke a tsakiyar su.
10 Yesu ya tashi tsaye ya ce da ita, “mace, ina masu zargin ki? Ba wanda ya kashe ki?
11 Ta ce, “Ba kowa, Ubangiji” Yesu ya ce, “Ni ma ban kashe ki ba. Ki yi tafiyar ki, daga yanzu kada ki kara yin zunubi.”
Yahaya 8 in Litafi Mai-tsarki