Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 7:8-31 in Hausa

Help us?

Yahaya 7:8-31 in Litafi Mai-tsarki

8 Ku ku je wurin idin, ni ba zan je wurin idin ba domin lokacina bai yi ba tukuna.
9 Bayan da ya gaya masu wadannan abubuwa, ya tsaya a cikin Gallili.
10 Amma bayan da 'yan'uwansa su ka tafi wurin idin shi ma ya tafi, amma a asirce ba a fili ba.
11 Saboda Yahudawa suna neman sa a wurin idin, su na cewa “Ina yake?”
12 Akwai maganganu dayawa a kansa cikin taron. Wadansu suna cewa, “shi mutumin kirki ne.” Wadansu kuma suna cewa, “A'a yana karkatar da hankalin jama'a.”
13 Amma duk da haka ba wanda ya yi magana a fili a kansa saboda suna jin tsoron Yahudawa.
14 Sa'anda aka kai rabin idin, sai Yesu ya shiga cikin haikali ya fara koyarwa.
15 Yahudawa suna mamaki suna cewa, “Yaya aka yi wannan mutum ya sami ilimi dayawa haka? Shi kuwa bai je makaranta ba.”
16 Yesu ya ba su amsa ya ce, “Koyarwata ba tawa ba ce, amma ta wanda ya aiko ni ce.”
17 Idan wani yana so ya yi nufinsa, za ya gane koyarwannan ko daga wurin Allah ta zo, ko ko tawa ce ta kaina.
18 Ko wanene yake maganar kansa, yana neman darajar kansa kenan, amma ko wanene ya nemi darajar wanda ya aiko ni, wannan mutum mai gaskiya ne, babu rashin adalci a cikin sa.
19 Ba Musa ya baku dokoki ba? Amma duk da haka ba mai aikata dokokin. Me yasa ku ke so ku kashe ni?
20 Taron suka ba shi amsa, “Ka na da aljani. Wanene yake so ya kashe ka?”
21 Yesu ya amsa ya ce masu, “Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi.
22 Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya.
23 Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
24 Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci.”
25 Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?”
26 Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba?
27 da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.”
28 Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, “Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba.
29 Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni.”
30 Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna.
31 Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce, “Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?”
Yahaya 7 in Litafi Mai-tsarki