Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 7:40-44 in Hausa

Help us?

Yahaya 7:40-44 in Litafi Mai-tsarki

40 Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, “Wannan lallai annabi ne.”
41 Wadansu suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma wadansu suka ce, “Almasihu zai fito daga Gallili ne.?
42 Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?”
43 Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi.
44 Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu.
Yahaya 7 in Litafi Mai-tsarki