Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 7:25-52 in Hausa

Help us?

Yahaya 7:25-52 in Litafi Mai-tsarki

25 Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?”
26 Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba?
27 da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.”
28 Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, “Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba.
29 Ni na san shi domin daga wurinsa na fito, kuma shine ya aiko ni.”
30 Suna kokari su kama shi, amma ba wanda ya iya sa masa hannu domin sa'arsa ba ta yi ba tukuna.
31 Duk da haka wadansu dayawa a cikin taron suka bada gaskiya gare shi suka ce, “Sa'anda Kristi ya zo, zai yi alamu fiye da wadanda wannan mutum ya yi?”
32 Farisawa suka ji tattarmukan suna yin rada a kan wadannan abubuwa game da Yesu, Sai manyan malamai da Farisawa su ka aika jami'ai su kama shi.
33 Sa'annan Yesu yace ma su,” jimawa kadan ina tare ku, sa'annan in tafi wurin wanda ya aiko ni.
34 Za ku neme ni ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba.”
35 Yahudawa fa su ka cewa junan su, “Ina wannan mutum zai je inda ba za mu iya samun sa ba? Ko za ya tafi wurin Helinawa na warwatsuwa ya koyawa Helinawa?
36 Wace kalma ya ke fadi haka, 'za ku neme ni amma ba za ku same ni ba; inda na tafi, ba za ku iya zuwa ba'?”
37 To a rana ta karshe, babbar rana ta idin, Yesu ya mike ya yi magana da karfi cewa, “Idan kowa yana jin kishi, ya zo wuri na ya sha.
38 Shi wanda ya bada gaskiya gare ni kamar yadda nassi ya fadi, daga cikin sa rafukan ruwa na rai za su bulbulo.”
39 Amma ya fadi haka a kan Ruhu, wanda wadanda suka bada gaskiya gare shi za su karba; ba a ba da Ruhun ba tukuna, saboda ba a rigaya an daukaka Yesu ba.
40 Wadansu a cikin taron, sa'anda suka ji wadannan kalmomi, suka ce, “Wannan lallai annabi ne.”
41 Wadansu suka ce, “Wannan Almasihu ne.” Amma wadansu suka ce, “Almasihu zai fito daga Gallili ne.?
42 Ba nassi ya ce Almasihu zai fito daga cikin dangin Dauda daga Baitalami ba, daga kauyen da Dauda ya fito?”
43 Sai aka sami rabuwa a cikin taron saboda shi.
44 Da wadansun su sun kama shi, amma ba wanda ya sa masa hannu.
45 Sa'annan jami'an suka dawo wurin manyan Fristoci da Farisawa, wadanda suka ce,” me yasa ba ku kawo shi ba?”
46 Jami'an su ka amsa, “Ba mutumin da ya taba yin magana kamar haka.”
47 Farisawa suka amsa masu, “kuma an karkatar da ku?
48 Ko wani daga cikin mahukunta ya bada gaskiya gare shi, ko kuwa daga cikin Farisawa?
49 Amma wannan taro da basu san shari'a ba, la'anannu ne.”
50 Nikodimus ya ce masu, (shi wanda ya zo wurin Yesu da, daya daga cikin Farisawa),
51 “Ko shari'armu bata hana hukunta mutum ba, sai ta ji daga gare shi ta kuma san abin da ya aikata ba?”
52 Suka amsa masa suka ce, “kai ma daga Galili ka fito? Ka yi bincike ka gani ba annanbin da zai fito daga Galili.”
Yahaya 7 in Litafi Mai-tsarki