Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 7:21-28 in Hausa

Help us?

Yahaya 7:21-28 in Litafi Mai-tsarki

21 Yesu ya amsa ya ce masu, “Nayi aiki daya, dukan ku kuna mamaki da shi.
22 Musa ya baku kaciya, {ba kuwa daga Musa take ba, amma daga kakannin kakanni ta ke}, kuma a ranar Asabar kukan yi wa mutum kaciya.
23 Idan mutum ya karbi kaciya ranar Asabar, domin kada a karya dokar Musa, don me kuka ji haushi na saboda na mai da mutum lafiyayye sarai ranar Asabar?
24 Kada ku yi shari'a ta ganin ido, amma ku yi shari'a mai adalci.”
25 Wadansun su daga Urushalima suka ce, “wannan ba shine wannan da suke nema su kashe ba?”
26 Kuma duba, yana magana a fili, sannan ba wanda ya ce da shi komai. Ba zai yiwu ba mahukunta su sani cewa wannan Kristi ne, ko ba haka ba?
27 da haka, mun san inda wannan mutum ya fito. Amma sa'anda Kristi za ya zo, ba wanda zai san inda ya fito.”
28 Yesu yayi magana da karfi a haikali, yana koyarwa ya na cewa, “Kun san ni kuma kun san inda na fito. Ban zo domin kaina ba, amma wanda ya aiko ni mai gaskiya ne, ku kuwa baku san shi ba.
Yahaya 7 in Litafi Mai-tsarki