Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 7:1-6 in Hausa

Help us?

Yahaya 7:1-6 in Litafi Mai-tsarki

1 Bayan wadannan abubuwa Yesu ya zagaya cikin Gallili, saboda baya so ya shiga cikin Yahudiya domin Yahudawa suna shirin su kashe shi.
2 To Idin Bukkoki na Yahudawa ya kusa.
3 Sai 'yan'uwansa suka ce da shi, “ka tashi ka tafi Yahudiya, domin almajiranka su ga ayyukan da kake yi su ma.
4 Ba wanda ya ke yin wani abu a boye idan dai yana so kowa da kowa ya san shi. Da yake ka na yin wadannan abubuwa sai ka nuna kan ka a fili ga duniya.
5 Domin ko 'yan'uwansa ma basu bada gaskiya gare shi ba.
6 Yesu ya ce dasu, “lokaci na bai yi ba tukuna, amma ku koyaushe lokacin ku ne.
Yahaya 7 in Litafi Mai-tsarki