Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 6:5-12 in Hausa

Help us?

Yahaya 6:5-12 in Litafi Mai-tsarki

5 Da Yesu ya daga kai sai ya ga babban taro yana zuwa wurinsa, sai ya ce ma Filibus, “Ina za mu sayi gurasar da Mutanen nan za su ci?”
6 (Ya fadi haka ne domin ya gwada shi, saboda shi kansa ya san abin da zai yi.)
7 Filibus ya amsa masa, “gurasar dinari biyu ma ba zata ishi kowannensu ya samu ko kadan ba.”
8 Daya daga cikin almajiransa, wato Andarawus, dan'uwan Siman Bitrus, ya ce masa,
9 “Ga wani dan yaro nan da dunkule biyar na sha'ir, da kifi biyu. Amma menene wadannan za su yi wa mutane masu yawa?”
10 Yesu ya ce, “ku sa mutane su zauna.” (wurin kuwa akwai ciyawa.) Sai mazajen suka zauna, sun kai wajen dubu biyar.
11 Sai Yesu ya dauki gurasar, bayan da ya yi godiya, sai ya rarraba wa wadanda suke zaune. Haka kuma ya rarraba kifin gwargwadon abin da zai ishe su.
12 Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara.”
Yahaya 6 in Litafi Mai-tsarki