Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 6:25-71 in Hausa

Help us?

Yahaya 6:25-71 in Litafi Mai-tsarki

25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Mallam, yaushe ka zo nan?”
26 Yesu ya amsa masu, da cewa, “hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi.
27 Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa.”
28 Sai suka ce Masa, “Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah?
29 Yesu ya amsa, “Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko.”
30 Sai suka ce masa, “To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka?
31 Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, “Ya ba su gurasa daga sama su ci.”
32 Sa'an nan Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama.
33 Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya,”
34 Sai suka ce masa, “Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe.”
35 Yesu ya ce masu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba.
36 Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.
37 Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan.
38 Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
39 Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe.
40 Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe.
41 Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, “Nine Gurasar da ta sauko daga sama.”
42 Suka ce, “Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'?
43 Yesu ya amsa, ya ce masu, “Kada ku yi gunaguni a junanku.
44 Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe.
45 A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni.
46 Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban.
47 Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami.
48 Ni ne Gurasa ta rai.
49 Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu.
50 Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba.
51 Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya.”
52 Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, “Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci?
53 Sai Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba.
54 Dukan wanda ya ci nama na ya kuma sha jinina yana da rai Madawwami, ni kuwa zan tashe shi a ranar karshe.
55 Domin namana abinci ne na gaske, jinina kuma abin sha ne na gaskiya.
56 Duk wanda ya ci namana, ya kuma sha jinina yana zamne a ciki na, ni kuma a cikinsa.
57 Kamar yadda rayayyen Uba ya aiko ni, nake kuma rayuwa saboda Uban, haka ma wanda ya ci namana, zai rayu sabo da ni.
58 Wannan itace gurasar da ta sauko daga sama, ba irin wadda Ubanninku suka ci suka mutu ba. Dukan wanda ya ci gurasar zai rayu har abada.”
59 Yesu ya fadi wadan nan abubuwa a cikin majami'a sa'ad da yake koyarwa a Kafarnahum.
60 Da jin haka, da yawa daga cikin almajiransa suka ce, “Wannan Magana yana da karfi, wa zai iya jinta?”
61 Yesu, kuwa da yake ya sani a ransa da cewa almajiransa suna gunagunin wannan, sai ya ce masu, “Wannan ya zamar maku laifi?
62 Yaya Ke nan in kun ga Dan Mutum yana hawa inda yake a da?
63 Ruhu shine mai bayar da rai; Jiki ba ya amfana komai. Kalmomin da na fada maku ruhu ne, da kuma rai.
64 Amma fa akwai wadansun ku da ba su ba da gaskiya ba. Domin tun farko Yesu ya san wadanda ba su ba da gaskiya ba, da kuma wanda zai bashe shi.
65 Ya fada cewa, “shiyasa na gaya maku, ba mai iya zuwa wurina, sai ta wurin Uban.”
66 Bayan haka, da yawa daga cikin almajiransa suka koma da baya, ba su kara tafiya tare da shi ba.
67 Sai Yesu ya ce wa goma sha biyun, “ku ba kwa so ku tafi, ko ba haka ba?
68 Bitrus ya amsa masa ya ce, “Ya Ubangiji, gun wa za mu je? kai kake da maganar rai madawwami.
69 Mu kwa mun gaskata mun kuma sani kai ne mai tsarkin nan na Allah.”
70 Yesu ya ce masu, “Ba ni na zabe ku, goma sha biyu ba, amma dayanku Iblis ne?”
71 Wato yana magana akan Yahuda dan Siman Iskariyoti, shi kuwa daya daga cikin sha-biyun ne, wanda zai ba da Yesu.
Yahaya 6 in Litafi Mai-tsarki