Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 6:17-53 in Hausa

Help us?

Yahaya 6:17-53 in Litafi Mai-tsarki

17 Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.)
18 Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa.
19 Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita.
20 Amma ya ce masu, “Ni ne! kada ku firgita.”
21 Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci.
22 Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai.
23 Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya.
24 Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Mallam, yaushe ka zo nan?”
26 Yesu ya amsa masu, da cewa, “hakika, kuna nema na ne, ba don kun ga alamu ba, amma domin kun ci gurasar nan kun koshi.
27 Ku daina yin wahala a kan neman abinci mai lalacewa, sai dai a kan abinci mai dawwama wanda zai kaiku ga rai madawwami wanda Dan Mutum zai ba ku, domin Ubangiji Allah ya sa hatiminsa a kansa.”
28 Sai suka ce Masa, “Me za mu yi, domin mu aikata ayyukan Allah?
29 Yesu ya amsa, “Wannan shi ne aikin Allah: wato ku gaskata da wanda ya aiko.”
30 Sai suka ce masa, “To wace alama za ka yi, don mu gani mu gaskata ka?
31 Me za ka yi? Kakanninmu sun ci manna a jeji, kamar yadda aka rubuta, “Ya ba su gurasa daga sama su ci.”
32 Sa'an nan Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, ina gaya maku ba Musa ne ya ba ku gurasa nan daga sama ba, amma Ubana ne ya baku gurasa ta gaskiya daga sama.
33 Gurasar Allah itace mai saukowa daga sama mai kuma bada rai ga duniya,”
34 Sai suka ce masa, “Mallam, ka rika ba mu irin wannan gurasa kodayaushe.”
35 Yesu ya ce masu, “Ni ne gurasa mai ba da rai. Wanda ya zo wurina ba zai ji yunwa ba, wanda kuma ya gaskanta da ni ba zai kara jin kishi ba.
36 Amma na gaya maku cewa, hakika kun gan ni, duk da haka ba ku ba da gaskiya ba.
37 Duk wanda Uba ya bani zai zo gare ni, wanda kuwa ya zo gare ni ba zan kore shi ba ko kadan.
38 Gama na sauko daga sama, ba domin in bi nufin kaina ba, sai dai nufin wanda ya aiko ni.
39 Wannan shi ne nufin wanda ya aiko ni, kada in rasa ko daya daga cikin wadannan da ya bani, sai dai in tashe su a ranar karshe.
40 Gama wannan shi ne nufin Ubana, duk wanda yake ganin Dan ya kuma gaskata da shi zai sami rai madawwami, ni kuma zan tashe shi a ranar karshe.
41 Sai Yahudawa suka yi gunaguni akansa, domin ya ce, “Nine Gurasar da ta sauko daga sama.”
42 Suka ce, “Ba wannan ne Yesu Dan Yusufu, wanda Ubansa da Uwarsa mun san su ba? Ta yaya yanzu zai ce, 'Na ya sauko daga sama'?
43 Yesu ya amsa, ya ce masu, “Kada ku yi gunaguni a junanku.
44 Ba mai iya zuwa wurina sai dai in Uba wanda ya aiko ni ya jawo shi, ni kuwa zan tashe shi a rana ta karshe.
45 A rubuce yake cikin litattafan anabawa cewa, 'Dukkansu Allah zai koya masu'. Duk wanda ya ji ya kuma koya daga wurin Uba, ya kan zo gare ni.
46 Ba cewa wani ya taba ganin Uban ba, sai shi wanda yake daga wurin Allah - shine ya ga Uban.
47 Hakika, hakika, wanda ya bada gaskiya, yana da rai Madawwami.
48 Ni ne Gurasa ta rai.
49 Ubanninku sun ci manna cikin jeji, suka kuma mutu.
50 Ga gurasa da ta sauko daga sama, domin mutum ya ci daga cikinta ba kuwa zai mutu ba.
51 Ni ne gurasa mai rai da ya sauko daga sama. Duk wanda ya ci daga gurasar, zai rayu har abada. Wannan gurasar da zan bayar jiki na ne don ceton duniya.”
52 Sai Yahudawa suka fusata a tsakanin junansu suka kuma fara gardama, cewa, “Yaya mutumin nan zai iya bamu naman jikinsa mu ci?
53 Sai Yesu ya ce masu, “hakika, hakika, in ba ku ci naman jikin Dan mutum ba, ba ku kuma sha jininsa ba, ba za ku sami rai a cikin ku ba.
Yahaya 6 in Litafi Mai-tsarki