Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 6:12-25 in Hausa

Help us?

Yahaya 6:12-25 in Litafi Mai-tsarki

12 Da Mutanen suka ci suka kuma koshi, sai ya ce wa almajiransa, ku tattara gutsattsarin da suka rage, kada ya zama asara.”
13 Sai suka cika kwanduna goma sha biyu da gutsattsarin gurasar nan biyar da ya rage bayan da kowa ya ci.
14 Da jama'a suka ga alamar da ya yi, sai suka ce, “Hakika wannan shi ne annabin nan mai zuwa cikin duniya.
15 “Da Yesu ya gane suna shirin zuwa su dauke shi da karfi da yaji su nada shi sarki, sai ya sake komawa kan dutsen da kansa.
16 Da yamma ta yi, sai almajiransa suka gangara teku.
17 Suka shiga cikin jirgi, suka haye teku zuwa kafarnahum. (A lokacin duhu ya yi, Yesu kuwa bai riga ya iso wurinsu ba tukuna.)
18 Iska mai karfin gaske tana kadawa, kuma tekun yana hargowa.
19 Bayan da almajiran suka yi tuki na wajen kimanin mil ashirin da biyar ko talatin, sai suka hango Yesu yana tafiya a kan teku ya kuma kusa da jirgin, sai suka firgita.
20 Amma ya ce masu, “Ni ne! kada ku firgita.”
21 Sa'an nan suka yarda suka karbe shi a cikin jirgin, kuma nan da nan jirgin ya kai gacci.
22 Kashe gari, sauran taron da suke tsaye a dayan hayin tekun suka ga cewa babu wani jirgi a wajen sai dayan, Yesu kuma bai shiga ciki da almajiransa ba, amma almajiransa suka tafi su kadai.
23 Sai dai, akwai wadansu jirage da suka zo daga Tibariya kusa da wurin da taron suka ci gurasa bayan da Ubangiji ya yi godiya.
24 Sa'anda taron suka gane cewa Yesu da almajiransa ba su wurin, su da kansu su ka shiga cikin jiragen suka tafi Kafarnahum neman Yesu.
25 Da suka same shi a hayin tekun, suka ce masa, “Mallam, yaushe ka zo nan?”
Yahaya 6 in Litafi Mai-tsarki