Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 5:6-19 in Hausa

Help us?

Yahaya 5:6-19 in Litafi Mai-tsarki

6 Da Yesu ya gan shi yana kwance a wurin sai ya gane ya dade a wurin, sai ya ce masa, “Ko kana so ka warke?”
7 Sai mai rashin lafiyar ya amsa ya ce, “Malam, bani da kowa da zai sa ni a cikin tabkin idan ruwan ya motsa. Yayinda na ke kokari sai wani ya riga ni.”
8 Yesu ya ce masa,” Ka tashi ka dauki shimfidarka ka tafi.”
9 Nan dan nan Mutumin ya warke, ya dauki shimfidarsa ya tafi. Ranar kuwa Asabar ce.
10 Sai Yahudawa suka ce da wanda aka warkar din, “Ai, Asabar ce, bai kuwa halatta ka dauki shimfidarka ba.”
11 Sai ya amsa ya ce, “Ai wanda ya warkar da ni, shine ya ce mani 'Dauki shimfidarka, ka tafi.”
12 Suka tambaye shi, “wane mutum ne ya ce maka, 'Dauki shimfidar ka yi tafiya'?”
13 Sai dai, shi wanda aka warka din, ba san ko wanene ya warkar da shi ba, domin Yesu ya riga ya tafi aboye, saboda akwai taro a wurin.
14 Bayan haka, Yesu ya same shi a Haikalin, ya ce masa, “ka ga fa, ka warke. To, kada ka kara yin zunubi don kada wani abu da ya fi wannan muni ya same ka.”
15 Sai mutumin ya tafi ya gaya wa Yahuduwa cewa Yesu ne ya warkar da shi.
16 To saboda haka Yahudawa suka fara tsanantawa Yesu, don ya yi wadannan abubuwa ran Asabar.
17 Yesu kuwa ya amsa masu ya ce, “Ubana yana aiki har yanzu, ni ma ina aiki.”
18 Saboda haka, Yahudawa suka kara nema su kashe shi ba don ya keta Asabar kadai ba, amma kuma domin ya ce Allah Ubansa ne, wato yana maida kansa dai-dai da Allah.
19 Yesu ya amsa masu ya ce, hakika hakika, ina gaya maku, Dan ba ya yin kome shi kadai, sai abin da ya ga Uba yana yi.
Yahaya 5 in Litafi Mai-tsarki