Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 4:8-23 in Hausa

Help us?

Yahaya 4:8-23 in Litafi Mai-tsarki

8 Gama almajiransa sun tafi cikin gari don sayen abinci.
9 Sai ba-Samariyar tace masa, “Yaya kai da kake Bayahude kake tambaya ta ruwan sha, ni da nike 'yar Samariya?” Domin Yahudawa ba su harka da Samariyawa.
10 Sai Yesu ya amsa yace mata, “In da kin san kyautar Allah, da shi wanda yake ce da ke, 'Ba ni ruwan sha,' da kin roke shi, sai kuma ya ba ki ruwan rai.”
11 Matar tace masa, “Mallam, ga shi ba ka da guga, kuma rijiyar tana da zurfi. Ina za ka samu ruwan rai?
12 Ai ba ka fi Ubanmu Yakubu ba, ko ka fi shi, shi wanda ya ba mu rijiyar, shi kansa kuma ya sha daga cikin ta, haka kuma 'ya'yansa da shanunsa?”
13 Yesu ya amsa yace mata, “duk wanda ya sha daga wannan ruwan zai sake jin kishi,
14 amma duk wanda ya sha daga ruwa da zan ba shi ba zai sake jin kishi ba. Maimakon haka, ruwan da zan bashi zai zama mabulbular ruwa a cikinsa wanda ke bulbula zuwa rai madawwami.”
15 Matar tace masa, “Mallam, ka ba ni wannan ruwa yadda ba zan kara jin kishi ba ba kuma sai na zo nan don in dibi ruwa ba.”
16 Yesu ya ce mata, “Je, ki kira maigidanki ku zo nan tare.”
17 Matar ta amsa tace masa, “Ba ni da miji.” Yesu yace, “Kin fadi daidai da kika ce, 'ba ni da miji,'
18 domin kin auri mazaje har biyar, kuma wanda kike da shi yanzu ba mijin ki bane. Abinda kika fada gaskiya ne.”
19 Matar tace masa, “Mallam, Na ga kai annabi ne.
20 Ubaninmu sun yi sujada a wannan dutse, amma kun ce Urushalima ce wurin da ya kamata mutane su yi sujada.”
21 Yesu ya ce mata, “Mace, ki gaskata ni, cewa lokaci na zuwa wanda ba za ku yi wa Uban sujada ba ko akan wannan dutse ko a Urushalima.
22 Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu muna bauta wa abinda muka sani, gama ceto daga Yahudawa yake.
23 Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada.
Yahaya 4 in Litafi Mai-tsarki