Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 4:28-42 in Hausa

Help us?

Yahaya 4:28-42 in Litafi Mai-tsarki

28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen,
29 “Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?”
30 Suka bar garin suka zo wurinsa.
31 A wannan lokacin, almajiransa suna rokansa, cewa, “Mallam, ka ci.”
32 Amma ya ce masu, “ina da abinci da ba ku san komai akai ba.”
33 Sai almajiran suka ce da junansu, “Babu wanda ya kawo masa wani abu ya ci, ko akwai ne?”
34 Yesu ya ce masu, “Abincina shine in yi nufin wanda ya aiko ni, in kuma cika aikinsa.
35 Ba ku kan ce, 'akwai wata hudu tukuna kafin girbi ya zo ba?' Ina gaya maku, daga idanunku ku ga gonakin, sun rigaya sun isa girbi.
36 Shi wanda ke girbi yakan karbi sakamako ya kuma tattara amfanin gona zuwa rai na har abada, ta haka shi mai shuka da shi mai girbi za su yi farinciki tare.
37 Gama cikin wannan maganar take, 'Wani na shuka, wani kuma na girbi.'
38 Na aike ku ku yi girbin abinda ba ku yi aiki a kai ba. Wandansu sun yi aiki, ku kuma kun shiga cikin wahalarsu.
39 Yawancin Samariyawan da ke wannan birni suka gaskata da shi sabili da labarin matar data bada shaida, “Ya gaya mani duk abinda na taba yi.”
40 To sa'adda Samariyawa suka zo wurinsa, sai suka roke shi ya zauna tare da su, ya kuwa zauna wurin kwana biyu.
41 Wasu da dama kuma suka gaskata domin maganarsa.
42 Suka cewa matar, “Mun bada gaskiya, ba saboda maganar ki kadai ba, amma mu kanmu munji, yanzu kuma mun sani cewa wannan lallai shine mai ceton duniya.”
Yahaya 4 in Litafi Mai-tsarki