Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 4:22-29 in Hausa

Help us?

Yahaya 4:22-29 in Litafi Mai-tsarki

22 Ku kuna bauta wa abinda ba ku sani ba. Mu muna bauta wa abinda muka sani, gama ceto daga Yahudawa yake.
23 Sai dai, sa'a tana zuwa, har ma ta yi, wadda masu sujada na gaskiya za su yi wa Uba sujada a cikin ruhu da gaskiya, domin irin wadannan ne Uban ke nema su zama masu yi masa sujada.
24 Allah Ruhu ne, kuma mutanen da ke yi masa sujada, dole su yi sujada cikin ruhu da gaskiya.”
25 Matar ta ce masa, “Na san Almasihu na zuwa (wanda ake kira Kristi). Sa'adda ya zo, zai bayyana mana kowane abu.
26 Yesu ya ce mata, “Ni ne shi, wanda ke yi maki magana.”
27 A daidai wannan lokaci, almajiransa suka dawo. Suna ta mamakin dalilin da yasa yake magana da mace, amma babu wanda yace, “Me kake so?” Ko kuma, “Don me ka ke magana da ita?”
28 Sai matar ta bar tulunta, ta koma cikin gari, tace wa mutanen,
29 “Ku zo ku ga wani mutum wanda ya gaya mani duk wani abu da na taba yi. Wannan dai ba Almasihun bane, ko kuwa?”
Yahaya 4 in Litafi Mai-tsarki