Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 3:1-11 in Hausa

Help us?

Yahaya 3:1-11 in Litafi Mai-tsarki

1 akwai wani Bafarise da ake kira Nikodimu, shugaba a cikin Yahudawa.
2 Wannan mutum ya zo wurin Yesu da dare ya ce masa, “Rabbi, mun sani cewa kai malami ne da kazo daga wurin Allah, gama ba wanda zai iya yin wadannan alamu da kake yi sai idan Allah na tare da shi.”
3 Yesu ya amsa masa, “Hakika, hakika, idan ba a sake haifuwar mutum ba, ba zai iya ganin mulkin Allah ba.”
4 Nikodimu ya ce masa, “Yaya za a sake haifuwar mutum bayan ya tsufa? Ba zai iya sake shiga cikin cikin uwarsa kuma a haife shi ba, zai iya?”
5 Yesu ya amsa, “Hakika, hakika, idan ba a haifi mutum da ruwa da kuma Ruhu ba, ba zai iya shiga cikin mulkin Allah ba.
6 Abin da aka haifa ta wurin jiki, jiki ne, kuma abin da aka haifa ta wurin Ruhu, Ruhu ne.
7 Kada ka yi mamaki don na ce maka, 'dole a maya haifuwar ka.'
8 Iska takan hura duk inda ta ga dama. Ka kan ji motsin ta, amma ba ka san inda ta fito ko inda za ta tafi ba. Haka duk wanda aka haifa daga Ruhu.”
9 Nikodimu ya amsa yace masa, “Yaya wannan zai yiwu?”
10 Yesu ya amsa yace masa, “Kai malami ne a Israila amma ba ka san wadannan al'amura ba?
11 Hakika, hakika, ina gaya maka, muna fadin abubuwan da muka sani, kuma muna shaida abubuwan da muka gani. Duk da haka ba ku karbi shaidar mu ba.
Yahaya 3 in Litafi Mai-tsarki