Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 1:23-27 in Hausa

Help us?

Yahaya 1:23-27 in Litafi Mai-tsarki

23 Yace, “Ni murya ne, da ke kira cikin jeji, 'Ku daidaita hanyar Ubangiji,' kamar yadda annabi Ishaya ya fada.”
24 Su wadanda aka aika daga wurin Farisawa suke. Sai suka tambaye shi cewa,
25 “To don me kake baftisma idan kai ba Almasihu bane, ko Iliya, ko annabin?”.
26 Yahaya ya amsa masu, cewa, “Ina baftisma ne da ruwa. Amma a cikinku akwai wani tsaye wanda ba ku sani ba,
27 shi wanda ke zuwa bayana, wanda ko igiyar takalminsa ban isa in kwance ba.”
Yahaya 1 in Litafi Mai-tsarki