Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 13:22-38 in Hausa

Help us?

Yahaya 13:22-38 in Litafi Mai-tsarki

22 Almajiran suka kalli juna, suna juyayin ko akan wa yake magana.
23 Daya daga cikin almajiransa, wanda Yesu yake kauna, yana a teburi, jingine a kirjin Yesu.
24 Siman Bitrus ya ce wa almajirin, “ka fada mana ko akan wa ya ke magana.”
25 Sai ya sake jingina a kirjin Yesu, ya ce masa, “Ubangiji, wanene?”
26 Sannan Yesu ya amsa, “Shine wanda zan tsoma gutsuren gurasa in ba shi.” Sannan bayan ya tsoma gurasar, sai ya ba Yahuza Dan Siman Iskariyoti.
27 To bayan gurasar, sai shaidan ya shige shi, sai Yesu ya ce masa, “Abinda kake yi, ka yi shi da sauri.”
28 Babu wani a teburin da ya san dalilin dayasa ya fada masa wannan.
29 Wadansu sun yi tsamanin cewa, tun da Yahuza ne ke rike da jakkar kudi, Yesu ya ce masa, “Ka sayi abinda muke bukata don idin”, ko kuma ya bada wani abu domin gajiyayyu.
30 Bayan Yahuza ya karbi gurasar, sai ya fita nan da nan. Da daddare ne kuwa.
31 Bayan Yahuza ya tafi, Yesu ya ce, “Yanzu an daukaka Dan mutum, kuma an daukaka Allah a cikinsa.
32 Allah zai daukaka shi a cikin kansa, kuma zai daukaka shi nan da nan.
33 'Ya'ya kanana, ina tare da ku na wani gajeren lokaci. Zaku neme ni, kuma kamar yadda na fadawa Yahudawa, 'in da zan tafi ba za ku iya zuwa ba.' Yanzu kuma na fada maku wannan.
34 Ina baku sabuwar doka, ku kaunaci juna; kamar yadda na kaunace ku, haka kuma ku kaunaci juna.
35 Ta haka kowa zai san ku almajiraina ne, idan kuna kaunar juna.”
36 Siman Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina za ka?” Yesu ya amsa ya ce, “Inda za ni, ba zaka iya bi na ba yanzu, amma zaka bini daga baya.”
37 Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, don me ba zan iya binka a yanzu ba? Zan bada raina domin ka.”
38 Yesu ya amsa ya ce, “Za ka bada ranka domina? Lalle hakika, ina gaya maka, kafin zakara ya yi cara zaka yi musu na sau uku.”
Yahaya 13 in Litafi Mai-tsarki