Text copied!
Bibles in Hausa

Yahaya 12:34-46 in Hausa

Help us?

Yahaya 12:34-46 in Litafi Mai-tsarki

34 Taro suka amsa masa cewa, “Mun ji a cikin shari'a cewa Almasihu za ya kasance har abada. Yaya za ka ce, 'za'a daga dan mutum'? Wanene wannan dan mutum?”
35 Yesu ya ce masu, “Nan da lokaci kadan za ku kasance da haske, ku yi tafiya tun haske na tare da ku, kada duhu ya mamaye ku. Wanda ke tafiya cikin duhu, bai san inda za shi ba.
36 Ku gaskata ga haske tun yana tare da ku domin ku zama yayan haske”. Yesu ya fadi wadannan abubuwa sannan ya tafi ya boye masu.
37 Kodashike Yesu ya yi alamu da dama a gabansu, duk da haka ba su gaskata shi ba.
38 Saboda maganar annabi Ishaya ta cika, wadda ya ce, “Ubangiji, wa ya gaskata rahoton mu? Ga wa kuma hannun Ubangiji ya bayyana?
39 Saboda wannan dalili basu gaskata ba, gama Ishaya ya sake cewa,
40 ya makantar da su, ya kuma taurare zuciyarsu, saboda kada su gani da idanunsu, su kuma sami fahimta da zuciyarsu, su juyo wurina in warkar da su.
41 Ishaya ya fadi wadannan abubuwa ne domin ya hangi daukakar Yesu ya kuma yi magana game da shi.
42 Amma duk da haka, dayawa cikin shugabanni suka gaskata Yesu. Amma saboda farisawa, basu shaida shi a sarari ba, domin kada a kore su daga majami'a.
43 Suna son yabo daga mutane fiye da yabon dake zuwa daga Allah.
44 Yesu ya yi magana da babbar murya, ya ce, “Wanda ya gaskata ni, ba ni yake gaskatawa kadai ba, amma kuma yana gaskata wanda ya aiko ni,
45 kuma wanda ke gani na, yana ganin shi wanda ya aiko ni.
46 Na zo ne a matsayin haske a duniya, saboda duk wanda ya gaskata da ni ba za ya yi tafiya cikin duhu ba.
Yahaya 12 in Litafi Mai-tsarki