Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 7:10-19 in Hausa

Help us?

Romawa 7:10-19 in Litafi Mai-tsarki

10 Dokar wadda ta kamata ta kawo rai, sai na same ta matacciya.
11 Domin zunubin, ya dauki zarafi ta wurin dokar, ya rude ni, kuma ta wurin dokar ya kashe ni.
12 Domin haka, shari'ar na da tsarki, dokar na da tsarki, adalci da kuma kyau.
13 To abu mai kyau ya zamar mani mutuwa kenan? ba zai taba zama haka ba. Amma zunubi, domin ya nuna shi zunubi ne ta wurin abin da ke mai kyau, sai ya kawo mutuwa a cikina. Wannan ya kasance haka ne domin ta wurin dokar, zunubi ya zama cikakken zunubi.
14 Domin mun san shari'a mai Ruhaniya ce, amma ni ina cikin jiki. An sai da ni karkashin bautar zunubi.
15 Domin ni ma ban fahimci abin da nake aikatawa ba. Domin abin da nake so in aikata, ba shi nake aikatawa ba, kuma abin da bana so, shi nake aikatawa.
16 Amma idan na aikata abin da bana so, na amince da shari'a kenan, cewar shari'a nada kyau.
17 Amma yanzu ba ni ke aikata abin ba, amma zunubi da ke zaune a cikina.
18 Domin na san a cikina, wato cikin jikina, babu wani abu mai kyau. Domin marmarin aikata abu mai kyau na tare da ni, amma ba ni iya aikatawa.
19 Domin abu mai kyau da na ke so in aikata bana iyawa, amma muguntar da ba na so ita na ke aikatawa.
Romawa 7 in Litafi Mai-tsarki