Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 5:15-21 in Hausa

Help us?

Romawa 5:15-21 in Litafi Mai-tsarki

15 Amma kyautar ba kamar keta umarnin take ba. Domin in sabo da laifin mutum dayan nan ne, da yawa suke mutuwa, haka ma alherin sa da baiwarsa ta wurin mutum dayan nan, Yesu Almasihu, sai baiwar ta wadata zuwa ga masu yawa.
16 Domin kyautar ba kamar sakamakon wannan da yayi zunubin bace. Ta haka din nan ne, hukuncin nan mai tsanani ya zo sabo da zunubin mutum dayan. Har yanzu dai, wannan baiwa ta yanci ta zo ne bayan laifuffuka masu yawa.
17 Domin, idan sabo da laifin mutum dayan nan ne, mutuwa ta mallake, saboda dayan, haka ma wadanda suka karbi alheri mai yawa da kuma baiwar adalci ta wurin ran, Yesu Almasihu.
18 Don haka, kamar yadda zunubin dayan ya sa hukunci ya zo kan dukka, haka ma aikin adalci na dayan zai kawo barata da rai ga mutane masu yawa.
19 Kuma kamar yadda rashin biyayyar dayan ta sa mutane masu yawan gaske su zama masu zunubi, haka ma ta biyayyar dayan mutane da yawan gaske za su sami adalci.
20 Amma shari'a ta zo, inda ta sa zunubi ya habaka. Amma inda zunubi ya habaka, alheri ma ya habaka ribin ribi.
21 Wannan ya faru ne, don kamar yadda zunubi yai mallaka zuwa mutuwa, haka kuma alheri ya mallaka zuwa adalci da rai na har abada ta wurin Yesu Almasihu Ubangijin mu.
Romawa 5 in Litafi Mai-tsarki