Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 5:1-10 in Hausa

Help us?

Romawa 5:1-10 in Litafi Mai-tsarki

1 Tun da shike mun sami barata, sabili da bangaskiya, mun sami salama tare da Allah ta wurin Yesu Almasihu.
2 Ta wurin sa kuma mun sami iso zuwa ga alheri inda muke tsayawa albarkacin bangaskiyarmu. Muna murna da gabagadin da Allah ya ba mu game da abin da zai faru, gabagadin da zamu dandana nan gaba cikin daukakar Allah.
3 Ba kuwa haka kadai ba, amma muna murna da shan wahalolinmu. Mun san cewa shan wuya na haifar da
4 Jimiri, Jimiri kuma na kawo amincewa, amincewa na kawo gabagadi game da abin da zai zo nan gaba.
5 Wannan gabagadi wato begen da muke da shi baya kunyatarwa, domin kuwa an kwarara mana kaunar Allah a cikin zuciyarmu ta wurin Ruhu Mai Tsarki, da aka ba mu.
6 Domin kuwa ko yayin da muke raunana, Almasihu ya mutu a lokacin da ke dai dai domin marasa ibada.
7 To ai kuwa yana da wuya kwarai wani mutum ya yarda ya mutu don mutumin kirki ma. Watakila, wani na iyayin kasada ya yarda ya mutu don nagarin mutum.
8 Amma Allah ya tabbatar mana da kaunarsa a gare mu, don kuwa tun muna masu zunubi, Almasihu ya mutu domin mu.
9 Balle ma yanzu, da muka barata ta wurin jininsa, za mu sami tsira daga fushin Allah.
10 Domin kuwa, in tun muna makiya, aka sulhunta mu da Allah ta wurin mutuwar Dansa, balle ma, yanzu da muka sami sulhu, zamu sami tsira ta wurin ransa.
Romawa 5 in Litafi Mai-tsarki