Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 3:4-21 in Hausa

Help us?

Romawa 3:4-21 in Litafi Mai-tsarki

4 Bazai taba zama haka ba. Maimakon haka, bari Allah ya zama mai gaskiya, ko da kowanne mutum makaryaci ne. Kamar yadda aka rubuta, “Domin a nuna kai mai adalci cikin maganganunka, kuma kayi nasara a lokacin da aka kawo ka gaban shari'a.”
5 Amma idan rashin adalcinmu ya nuna adalcin Allah, to me zamu ce? Allah ba marar adalci ba ne, wanda ke aiwatar da fushinsa, ko kuwa? Ina magana bisa ga tunanin mutuntaka.
6 Bazai taba zama haka ba. Domin idan haka ne ta yaya Allah zai shar'anta duniya?
7 Amma idan gaskiyar Allah ta wurin karyata ta habaka yabonsa, To me yasa ake shar'anta ni a matsayin mai zunubi?
8 To me zai hana ace kamar yadda ake fadin zancen karya a kanmu, wasu kuma sun dauka cewa mun fadi hakan, “Bari muyi mugunta, domin nagarta tazo?” Hukuncin su halal ne.
9 To me kenan? Zamu ba kanmu hujja ne? ko kadan. Domin mun riga munyi zargin yahudawa da hellinawa, da cewar dukkansu, suna karkashin zunubi.
10 Kamar yadda aka rubuta, babu wani mai adalci, babu ko daya.
11 Babu wani mai fahimta. Babu wani mai neman Allah.
12 Dukansu sun kauce hanya, dukansu gaba daya sun zama marasa amfani. Babu mai aikin nagarta, a'a, babu ko da guda daya.
13 Makogwaronsu a bude yake kamar kabari. Harsunansu na dauke da cuta. Dafin macizai na karkashin lebunansu.
14 Bakunansu cike suke da la'ana da daci.
15 Sawayensu na saurin zuwa zubar da jini.
16 Tafarkinsu wahala ce da lalacewa.
17 Wadannan mutane basu san hanyar salama ba.
18 Babu tsoron Allah a idanunsu.”
19 To mun san dai duk abin da shari'a tace, shari'a na magana ne da wadanda ke karkashinta, domin a rufe kowanne baki, domin dukan duniya ta bada amsa a gaban Allah.
20 Domin a gabansa babu wanda zai barata ta wurin ayukan shari'a. Domin ta wurin shari'a ne sanin zunubi yazo.
21 Amma yanzu ba tare da shari'a ba an bayyana sanin adalcin Allah, wanda shari'a da annabawa suke shaidawa.
Romawa 3 in Litafi Mai-tsarki