Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 1:17-23 in Hausa

Help us?

Romawa 1:17-23 in Litafi Mai-tsarki

17 Domin a cikin ta adalcin Allah ya bayyana daga bangaskiy zuwa bangaskiya, kamar yadda yake a rubuce, “Mai adalci zai rayu ne tawurin bangaskiya.”
18 Domin fushin Allah ya bayyana ne daga sama gaba da rashin ibada da rashin adalci na yan'adam, wadanda suke danne gaskiya ta wurin rashin adalcin su.
19 Dalili kuwa abinda yakamata a sani game da Allah a bayyane ya ke a gare su. Domin kuwa Allah ya bayyana masu shi a zahiri.
20 Domin al'amuransa da ba'a iya gani a bayyane suke tun halittar duniya. A na iya gane su ta wurin halitatattun abubuwa. Wadannan al'amura kuwa sune madawwamin ikonsa da Allahntakarsa. Sakamakon haka, wadannan mutane ba su da hujja.
21 Dalili kuwa, koda suna jin sun san Allah, amma basu darajanta shi a matsayin Allah ba, ko kuma su nuna masa godiya. Maimakon haka, suka zama wawaye a cikin tunaninsu, zukatansu marasa tunani sun duhunta.
22 Suna daukar kansu akan masu hikima ne su, amma sai ga su sun zama wawaye.
23 Sun musanya daukakar Allah madawwami da ta kamannin abubuwan da basa dawwama, kamar mutum, da tsuntsaye, da dabbobi masu kafafu hurhudu, da masu jan ciki.
Romawa 1 in Litafi Mai-tsarki