Text copied!
Bibles in Hausa

Romawa 15:5-16 in Hausa

Help us?

Romawa 15:5-16 in Litafi Mai-tsarki

5 Yanzu Allah mai hakuri da karfafawa ya baku zuciya daya ta zaman tare da juna bisa ga halin Yesu Almasihu.
6 Domin ya yi haka ne da zuciya daya domin ku yi yabo da bakinku daya.
7 Domin ku karbi juna, kamar yadda Yesu ma ya karbe ku domin a daukaka Allah.
8 Saboda na ce an mai da Almasihu bawan kaciya a madadin gaskiyar Allah. Ya yi wannan ne don a tabbatar da alkawarai da aka ba kakanin kakaninmu.
9 Domin Al'umai su daukaka Allah saboda jinkansa, kamar yadda ya ke a arubuce, “Domin ta haka zan yabe ka cikin Al'umai in yi wakar yabon sunanka.”
10 Kuma an ce. “Ku yi faranciki, ku Al'ummai tare da mutanensa.”
11 Kuma.” Ku yabi Ubangiji, ku dukan Al'ummai; bari dukan mutane su yabe shi.”
12 Kuma, Ishaya ya ce “Za a sami tsatson Yessi, wanda zai tashi ya yi mulki a kan Al'umai, Al'umai za su sami karfin hali a cikinsa.”
13 Yanzu Allah mai karfafawa ya cika ku da dukkan farin ciki salama, saboda da bangaskiyarku, domin ku sami cikkakiyar karafafawa, ta wurin ikon Ruhu Mai Tsarki.
14 Ni kaina na amince da ku, yan'uwa. Kuma na amince cewa ku da kanku kuna cike da alheri, cike da dukkan sani. Na amince cewa za ku sami zarafi ku gargadi juna.
15 Amma ina rubuta maku da gabagadi kan wadansu abubuwa, domin in tunasheku, saboda baiwar da aka bani daga wurin Allah.
16 Cewa baiwar ta sa na zama bawan Almasihu Yesu da aka aika ga Al'ummai, limami na bisharar Allah. Zan yi wannan saboda baikon Al'ummai ya zama karbabbe, kuma kebbabe ga Allah ta wurin Ruhu Mai Tsarki.
Romawa 15 in Litafi Mai-tsarki