Text copied!
Bibles in Hausa

Markus 9:28-47 in Hausa

Help us?

Markus 9:28-47 in Litafi Mai-tsarki

28 Da Yesu ya shiga gida, sai almajiransa suka tambaye shi a kadaice, me ya sa muka kasa fitar da shi?”
29 Ya ce masu, “Ai, irin wannan ba ya fita sai da addu'a.”
30 Sai suka ratsa cikin Galili, amma ba ya son kowa ya san inda suke.
31 Da yake koyar da almajiransa, ya ce masu lokaci na zuwa da za'a ba da Dan mutum a hannun mutane, za su kuwa kashe shi, sa'adda aka kashe shi kuma, bayan kwana uku zai tashi.
32 Amma fa ba su fahimci maganar ba, suna kuma jin tsoron tambayarsa.
33 Sai suka zo kafarnahum. A lokacin da ya ke cikin gida, ya tambayi Al'majiransa, Menene ku ke magana a kansa a hanya?
34 Amma suka yi shiru. don suna gardama da junansu akan hanya, a kan wane ne mafi girma.
35 Sai ya zauna, ya kira al'majiransa goma sha biyu, yace masu duk wanda ya ke so ya zama na fari, dole ya kankantar da kansa, sa'annan ya bautawa sauran duka.
36 Sai ya dauko karamin yaro a hannunsa ya sa shi a tsakiyarsu. Ya rumgome shi a kafadarsa ya ce masu.
37 Dukan wanda ya karbi dan karamin yaron nan a cikin sunana ni ya karba, kuma dukan wanda ya karbi wani, ni ya karba, bai kuma karbeni ni kadai ba, duk da wanda ya aiko ni.”
38 Sai Yahaya ya ce masa, Malam mun ga wani yana fitar da aljanu da sunanka mun yi kokari mu hana shi domin ba ya tare da mu.
39 Sai Yesu ya ce masu ku kyale shi domin babu wanda zai yi irin wannan babban aikin, sa'annan ya fadi wasu maganganu mara sa kyau a kanmu.
40 Duk wanda ba ya gaba da mu, na mu ne.
41 Duk wanda ya ba ku ruwa ku sha domin kuna na Almasihu, gaskiya nake fada maku ba za ya rasa ladansa ba.
42 Amma duk wanda ya sa kananan nan tuntube, ya fi kyau a rataya masa dutsen nika a jefa shi a cikin teku.
43 Idan har hannun ka zai sa ka yi tuntube, zai fi kyau ka yanke shi. Domin zai fi kyau ka shiga aljanna da hannu daya da ka shiga jahannama da hannu biyu.
44 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
45 Idan kafarka za ta sa ka yi tuntube, ka yanke ta ka yar. Zai fi kyau ka shiga aljanna da kafa daya da ka shiga jahannama da kafa biyu.
46 (Inda tsutsotsi basu mutuwa, wutar kuma bata mutuwa).
47 Idan idonka zai sa ka yi tuntube, ka kwakule shi ka yar, domin gwamma ka shiga mulkin Allah da ido daya, da a jefa ka cikin wuta da idanu biyu.
Markus 9 in Litafi Mai-tsarki