Text copied!
Bibles in Hausa

Markus 8:9-25 in Hausa

Help us?

Markus 8:9-25 in Litafi Mai-tsarki

9 Akwai maza kimanin dubu hudu a wurin. Yesu ya sallame su.
10 Nan take, ya shiga jirgin ruwa da almajiransa zuwa shiyyar Dalmanuta.
11 Sai Farisawa suka zo suka fara gardama da shi. Suna nema ya nuna masu alama daga sama, domin su gwada shi.
12 Ya ja numfashi a ruhunsa yana cewa, “Don me wannan tsarar tana neman alama. Hakika ina gaya maku, babu wata alama da za a ba wannan tsarar.”
13 Sai ya bar su ya sake shiga jirgin zuwa hayin tafkin.
14 A lokacin nan, almajiransa sun manta su dauki gurasa. Domin gurasa daya ce tak a garesu cikin jirgin ruwan.
15 Ya gargade su, “ku yi hattara da yisti na Farisawa da Yisti na Hirudus.”
16 Almajiran suka fara tattaunawa a tsakaninsu, “Saboda ba mu da gurasa ne.”
17 Yesu yana sane da wannan, sa'annan ya ce masu, “Don me kuke tattaunawa akan rashin gurasa? Har yanzu baku gane ba? Har yanzu ba ku da sane? Ko zuciyar ku ta duhunta ne?”
18 Kuna da idanu, ba ku gani? Kuna da kunnuwa, ba ku ji? Ba ku tuna ba?
19 Da na kakkarya gurasar a cikin mutane dubu biyar, kwanduna nawa kuka samu ragowa? Suka ce masa, “Goma sha biyu.”
20 Kuma da na kakarya gurasa bakwai a cikin mutane dubu hudu, kwanduna nawa kuka dauka cike da ragowar? Suka ce masa, “bakwai.”
21 Ya ce masu, “har yanzu baku gane ba?”
22 Sun zo Baitsaida. Mutanen wurin suka kawo masa wani makaho, sai suka roke shi ya taba shi.
23 Yesu ya rike hanun makahon, ya jagorance shi zuwa bayan kauyen. Da ya tofa yawunsa a idon mutumin, kuma ya dora hanunsa akan mutumin, sai ya tambaye shi “kana ganin wani abu kuwa?”
24 Ya daga ido sai ya ce, “ina ganin mutane na tafiya kamar itatuwa.”
25 Ya sake dora masa hannu a idanuwansa, mutumin ya bude idanuwansa, sai ya fara ganin gari da kyau.
Markus 8 in Litafi Mai-tsarki