Text copied!
Bibles in Hausa

Markus 6:7-25 in Hausa

Help us?

Markus 6:7-25 in Litafi Mai-tsarki

7 Ya kira almajiransa su goma sha biyu, ya aike su biyu-biyu, ya ba su iko a kan aljanu,
8 ya dokace su kada su dauki komai tare da su domin wannan tafiya, sai dai sanda kadai. Kada su dauki abinci ko jaka ko kudi a cikin aljihunsu,
9 sai dai su sa takalmi kadai, kada su sa taguwa biyu a jikinsu.
10 Ya ce da su, idan ku ka shiga wani gida sai ku zauna a gidan har lokacin da za ku tashi.
11 Idan ku ka je wani gari aka ki karbar ku, ku karkabe kurar da ke kafufunku ta zama shaida kan mutanen garin.
12 Sai suka tafi suka yi ta shela ga mutane cewa su tuba daga zunubansu.
13 Sun fitar da aljanu da yawa, suka shafawa mutane da yawa mai suka warkar da su.
14 Sarki Hirudus ya ji wannan, gama sunan Yesu ya zama sananne a wurin kowa da kowa. Wadansu suna cewa Yahaya mai yin baftisma ne ya tashi daga matattu shi ya sa ake yin wadannan ayyukan al'ajibi ta wurinsa.
15 Wadansu kuma suna cewa, “Iliya,” Har yanzu wadansu suna cewa daya “daga cikin annabawa ne na da can.”
16 Sa'adda Hirudus ya ji wannan sai ya ce, “Yahaya wanda na fillewa kai shine ya tashi.”
17 Saboda Hirudus ne ya sa aka kama Yahaya aka kulle shi a kurkuku saboda Hirodiya (matar Filibus dan'uwansa), domin ya aure ta.
18 Saboda Yahaya ya gaya wa Hirudus cewa bai halarta ya auri matar dan'uwansa ba.
19 Sai ita Hirodiya ta yi kudurin ta kashe Yahaya amma bai yiwu ba.
20 Domin Hirudus yana jin tsoron Yahaya, domin ya sani shi mai adalci ce, mai tsarki kuma. Domin haka Hirudus bai so wani abu ya faru da Yahaya ba, amma ya kan fusata idan ya ji wa'azin yahaya. Duk da haka da fari ciki yakan saurare shi.
21 Amma sai dama ta samu inda Hirodiya za ta iya yin abin da ta ke so ta yi. A lokacin kewayowar ranar haihuwar sa, sai Hirudus ya shirya liyafa domin manyan da ke aiki tare da shi a cikin gwamnatin sa, da shugabannin da ke cikin Galili.
22 Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, “ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi”.
23 Ya rantse mata da cewa” Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne”
24 Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, “me zan ce ya bani?” Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma.
25 Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, “Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire.”
Markus 6 in Litafi Mai-tsarki