Text copied!
Bibles in Hausa

Markus 6:22-55 in Hausa

Help us?

Markus 6:22-55 in Litafi Mai-tsarki

22 Diyar Hirodiya ta zo ta yi masu rawa, rawarta kuwa tagamshi Hirudus da bakinsa. Sarki ya ce da yarinyar, “ki tambayi duk abin da ki ke so ni kuwa zan ba ki shi”.
23 Ya rantse mata da cewa” Ko menene ki ka ce ki na so, ko da rabin mulkina ne”
24 Sai ta fita ta je ta tambayi mamarta, “me zan ce ya bani?” Sai ta ce kan Yahaya Mai Yin Baftisma.
25 Sai ta dawo da sauri cikin dakin taro wurin sarki ta ce da shi, “Ina so ka ba ni kan Yahaya Mai Yin Baftisma a cikin tire.”
26 Sarki ya damu kwarai, amma saboda ya yi alkawari ga kuma ofisoshinsa, ba dama ya ce a'a.
27 Sai sarki ya aiki wani soja ya ba shi ummurni ya je ya kawo kan Yahaya. Sojan ya je ya fillo kan sa daga cikin kurkuku.
28 Ya kawo kan a cikin tire ya ba yarinyar, yarinyar kuma ta kai wa mamarta.
29 Da almajiran su ka ji labari, suka zo suka dauki gawarsa suka rufe a cikin kabari.
30 Almajiran suka zo wurin Yesu, suka fada masa dukkan abin da suka yi da abin da suka koyar.
31 Sai ya ce da su “ku je cikin kebabben wuri domin ku huta kadan,” domin mutane suna ta kaiwa da komowa, ba su sami damar hutawa ba balle su ci abinci
32 Sai suka tafi kebabben wuri a cikin jirgin ruwa su kadai.
33 Amma mutane da yawa sun gansu suna tafiya sun kuma gane su, sai suka fito daga cikin dukan garuruwa da gudu har su ka kai wurin kafin su zo.
34 Sa'adda suka zo bakin gaba Yesu ya ga taron mutane da yawa sai ya ji tausayinsu domin sun yi kamar tumakin da ba da mai kiwo. Sai ya cigaba da koya masu abubuwa da yawa.
35 Sa'adda yamma ta yi, almajiran sa suka zo suka ce da shi, “wurinnan kebabben wuri ne kuma ga lokaci ya tafi.
36 Ka sallami mutanen nan domin su shiga cikin garuruwa da kauyuka da ke kusa domin su sayi abin da zasu ci.
37 Amma sai ya ba su amsa ya ce, “Ku ku basu abinci su ci mana”. Sai suka ce da shi, “ma iya zuwa mu sawo gurasa ta sule dari biyu mu basu su ci?”
38 Sai ya ce dasu, “Dunkulen gurasa guda nawa kuke dasu? Kuje ku gani.” Dasuka gano sai suka ce da shi, dunkule biyar ne da kifi guda biyu.”
39 Sai ya ba da umarni mutanen su dukka su zauna a kan danyar ciyawa.
40 Suka zauna kungiya kungiya wadansu su dari wadansu hamsin.
41 Sai ya dauki dunkulen gurasa guda biyar da kifi guda biyu, ya ta da kansa sama, yasa albarka, ya kakkarya dunkulen gurasan, ya ba almajiran domin su rabawa taron jama'a duka.
42 Dukansu suka ci suka koshi.
43 Suka tattara gutsattsarin gurasar suka cika kwanduna guda goma sha biyu da gutsattsarin da kuma gutsattsarin kifin.
44 Mutanen da suka ci gurasar sun kai mutum dubu biyar.
45 Nan da nan ya ce almajiran sa su hau jirgin ruwa su yi gaba kafin ya zo, su je Baitsaida. Shi kuma ya tsaya domin ya sallami taron mutanen.
46 Bayan da suka tafi shi kuma ya hau kan dutse domin ya yi addu'a.
47 Har yamma ta yi jirgin ruwan ya na tsakiyar rafi shi kuma yana kan tudu shi kadai.
48 Ya gansu suna wahala gama iska ta hana su tafiya. Wajan karfe hudu na asuba sai ya tawo wurin su yana tafiya a kan ruwa, yana so ya wuce gaban su.
49 Sa'adda suka gan shi ya na tafiya a kan ruwa suka yi tsammani fatalwa ce, suka yi ihu,
50 gama su duka sun gan shi, tsoro ya kama su. Sai nan da nan ya yi magana dasu ya ce, “Ku karfafa ni ne! kada ku ji tsoro!”
51 Ya shiga cikin jirgin ruwan tare dasu, sai iska ta dena bugawa. Sai suka yi mamaki kwarai.
52 Gama basu gane batun dunkulen ba. Maimakon haka, sai zukatansu suka taurare.
53 Sa'adda suka haye su zo kasar Janisarita suka sa wa jirgin sarka.
54 Su na fitowa daga cikin jirgin kenan, mutane suka gane cewa Yesu ne.
55 Mutane suka ruga cikin yankin su, suka kawo marasa lafiya a bisa shinfidun su zuwa wurinsa, dukan inda suka ji yana zuwa.
Markus 6 in Litafi Mai-tsarki