Text copied!
Bibles in Hausa

Markus 5:17-29 in Hausa

Help us?

Markus 5:17-29 in Litafi Mai-tsarki

17 Mutanen suka roke shi ya fita daga yankin kasarsu.
18 Shi mutumin da aljanu ke iko da shi, sa'adda ya ga Yesu zai shiga cikin jirgin ruwa ya tafi, ya roki Yesu da ya bi shi.
19 Amma Yesu bai yarda masa ba. Ya ce masa ka tafi gidanku, wurin mutanenka ka gaya ma su alherin da Ubangiji ya yi maka.
20 Mutumin ya shiga cikin Dikafolis yana shaidar babban abin da Yesu ya yi masa, dukansu suka cika da mamaki.
21 Sa'adda Yesu ya sake ketaren kogin zuwa daya gefen, acikin jirgin, sai taron jama'a suka keweye shi, a gefen tekun.
22 Sai wani daya daga cikin shugabannin Majami'a mai suna Yayirus, ya zo, wurinsa sa'adda ya ganshi ya durkusa a gabansa.
23 Ya yi ta rokonsa, yana cewa, “Diya ta ba ta da lafiya har ma ta kusa mutuwa. Ina rokonka mu je gida na ka dora ma ta hannu domin ta warke. ta rayu.”
24 Sai ya tafi tare da shi, babban taro suka biyo shi har ma suna matse shi.
25 Akwai wata mace wadda ta ke zubar jini ta kai tsawon shekara goma sha biyu.
26 Ta sha wahala kwarai da gaske ta je wurin likitoci da yawa ta kashe kudi sosai, amma ba ta warke ba abin ma sai karuwa ya ke yi.
27 Ta ji labarin Yesu. Sai ta biyo bayansa yana tafiya cikin taro, ta taba habar rigarsa.
28 Domin ta ce “Idan dai na taba ko da habar rigarsa zan warke.”
29 Da dai ta taba shi sai zubar jinin ta ta tsaya, ta ji a jikin ta ta warke, daga damuwarta.
Markus 5 in Litafi Mai-tsarki