Text copied!
Bibles in Hausa

Markus 4:24-39 in Hausa

Help us?

Markus 4:24-39 in Litafi Mai-tsarki

24 Sai ya ce masu, ku mai da hankali a kan abin da kuka ji, Mudun da ka auna, da shi za a auna maka, har ma a kara maka.
25 Domin mai abu akan karawa, marar abu kuma za a karba daga wurinsa a kuma karawa mai shi.”
26 Sai ya ce, “Mulkin Allah kamar mutum yake mai yafa iri a kasa.
27 A kwana a tashi har irin ya tsiro, ya girma bai kuwa san ta yaya aka yi ba.
28 Kasa da kanta, takan ba da amfani, tsiro shine ne na farko,
29 Sai kai, sa'anan sai kwaya mai kwari. Sa, adda amfani ya nuna, sai ya sa lauje ya yanke nan da nan, wato kaka ta yi kenan.”
30 Ya kuma ce, “Da me za mu kwatanta Mulki Allah? ko kuwa da wane misali za mu misalta shi?
31 Kamar kwayar zarra yake wadda, in an shuka ta, ko da yake ita ce mafi kankanta cikin kwayoyi a duniya.
32 Duk da haka in an shuka ta, sai ta yi girma fiye da duk sauran ita-tuwan da ke a jeji tayi manyan rassa, har tsuntsaye su iya yin sheka arassanta.”
33 Da misalai da yawa, irin wadannan ya yi masu Magana, dadai gwargwadon ganewarsu,
34 ba ya fada masu kome sai da misali, amma a kebe, yakan bayyana wa almajiransa dukan abu.
35 A ranan nan da yama ta yi yace masu “Mu haye wancan ketaren.”
36 Sai suka bar taron, suka tafi tare da shi acikin cikin jirgin. wadansu jirage kuma na tare da shi.
37 Sai babban hadari da iska mai karfi ya taso, rakuman ruwa kuma na ta girgizawa cikin jirgin, har jirgin ya cika.
38 Yesu kuwa na daga karshen bayan jirgin a kan kujera, yana barci, sai suka tashe shi, suka ce masa “Malam za mu hallaka ba ka kula ba?”
39 Sai ya farka, ya tsawata wa Iskar. Ya kuma ce wa ruwan tekun, “Ka natsu! ka yi shiru!” Sai Iskar ta kwanta, wurin duk ya yi shiru.
Markus 4 in Litafi Mai-tsarki