Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 9:31-62 in Hausa

Help us?

Luka 9:31-62 in Litafi Mai-tsarki

31 Suka bayyana da daraja kewaye da su, suka yi magana da Yesu a kan tafiyarsa wadda za ta zo ba da dadewa ba a cikin Urushalima.
32 Bitrus da almajiran da suke tare da shi barci mai nauyi ya dauke su. Sa'adda suka farka sai su suka ga daukakar Yesu; kuma suka ga mutanen su biyu da ke tsaye tare da shi.
33 Sa'adda Musa da Iliya suke shirin su bar wurin Yesu, sai Bitrus ya ce, “Ya shugaba, ya yi kyau da muke a nan. Zai yi kyau mu yi runfuna uku, daya dominka, daya domin Musa, daya kuma domin Iliya.” Amma hakika bai san abin da ya ke fadi ba.
34 Sa'adda yake fadin haka sai wani girgije ya zo ya rufe su. Sai suka ji tsoro sa'adda girgijen ya kewaye su.
35 Sai ga wata murya daga cikin girgijen tana cewa, “Wannan Dana ne wanda na zaba, ku ji shi.”
36 Sa'adda muryar ta gama magana, Yesu yana nan shi kadai. Suka yi shiru ba su iya cewa kome ba a kan abin da suka gani a kwanakin nan.
37 Washe gari, da suka sauko daga kan dutsen, sai taron mutane da yawa suka zo wurinsa.
38 Nan da nan, wani mutum daga cikin taron mutanen ya yi magana da karfi, “Mallam, kayi wani abu dominka taimaki da na, shi kadai ne gare ni.
39 Mugun ruhu ya kan hau kansa, ya sa shi ya yi ta magowa. Ya kan girjiza shi da karfi ya sa bakinsa ya yi ta kumfa. Da kyar ya ke rabuwa da shi, kuma ya kan ji masa ciwo ba kadan ba bayan da ya bar shi.
40 Na roki almajiran ka su umurci mugun ruhun ya fita daga cikinsa, amma ba su iya ba!”
41 Yesu, ya amsa, ya ce, “Ku karkatattun tsara marasa bangaskiya, har yaushe zan zauna da ku ina jimrewa da ku? “Kawo yaronka anan.”
42 Sa'adda yaron yake zuwa, sai mugun ruhun ya fyada yaron a kasa, ya jijjiga shi sosai. Amma Yesu ya tsauta wa mugun ruhun, ya warkar da yaron. Sa'annan ya mika yaron wurin mahaifinsa.
43 Dukansu suka yi mamaki da girman ikon Allah. Amma sa'anda suke ta yin mamaki a kan dukan al'ajiban da ya yi, ya ce da almajiransa,
44 “Ku saurara da kyau a kan abin da zan gaya maku, ba da dadewa ba za a bada Dan Mutum ga mutane.”
45 Amma almajiran ba su gane abin da yake nufi da haka ba, an hana su fahimta, domin kada su gane abin da ya ke nufi tukuna, kuma suna jin tsoron su tambaye shi.
46 Wani lokaci, almajiran suka fara gardama a tsakaninsu game da wanene za ya zama mafi girma a cikinsu.
47 Amma Yesu ya san abin da suke tunani a zuciyarsu, sai ya kawo dan karamin yaro ya tsaya a kusa da shi,
48 sai ya ce da su, “Idan wani ya karbi dan karamin yaro kamar wannan saboda ni, dai dai yake da ya karbe ni. Idan kuma wani ya karbe ni, ya karbi wanda ya aiko ni kenan. Wanda yake mafi kankanta a cikinku, shi ne mafi mahimmanci.”
49 Yahaya ya amsa yace, “Ya shugaba, mun ga wani mutum yana ba miyagun ruhohi umarni su fita daga cikin mutane da sunanka. Sai muka ce da shi ya dena yin haka saboda baya tare da mu.”
50 Amma Yesu ya ce, “Kada ku hana shi yin haka, domin dukan wanda ba ya gaba da ku, yana tare da ku.”
51 Sa'adda rana ta kusato da zai hawo zuwa sama, ya kudurta sosai zai tafi Urushalima.
52 Ya aiki wadansu manzanni su shirya wuri dominsa kafin ya zo. Suka shiga wani kauye a cikin kauyen Samariya domin su shirya masa wuri a can.
53 Amma mutanen can ba su karbe shi ba tun da ya ke Urushalima zai tafi.
54 Sa'adda biyu daga cikin almajiransa, wato Yakubu da Yahaya suka ga haka, suka ce, “Ubangiji, kana so mu umarci wuta ta sauko daga sama, ta hallaka su?”
55 Amma, ya juya ya tsauta masu.
56 Sai suka tafi wani kauye dabam.
57 Da suna cikin tafiya a kan hanya, sai wani mutum ya ce da shi, “Zan bi ka dukan inda za ka tafi.”
58 Yesu ya amsa masa, “Dila suna da ramuka a kasa inda za su shiga, tsuntsaye kuma suna da sheka, amma Dan Mutum ba shi da inda zai kwanta.”
59 Yesu, ya ce da wani mutumin kuma, “Ka biyo ni.” Amma mutumin ya ce, “Ubangiji, ka bari in koma gida in bizine mahaifina tukuna.”
60 Amma Yesu ya ce masa, “Ka bar matattu su bizine matattunsu; amma kai ka tafi ka yi wa mutane shelar mulkin Allah a ko'ina.”
61 Wani kuma ya ce, “Ubangiji zan tafi tare da kai, amma bari in je gida inyi ban kwana da mutanena tukuna.”
62 Yesu ya ce da shi, “Dukan wanda ya fara huda a gonarsa idan ya dubi baya, bai isa ya shiga mulkin Allah ba.”
Luka 9 in Litafi Mai-tsarki