Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 9:19-46 in Hausa

Help us?

Luka 9:19-46 in Litafi Mai-tsarki

19 Suka amsa, “Wadansu suna cewa, Yahaya mai yin Baftisma, wadansu suna cewa kai annabi Iliya ne, har yanzu wadansu suna cewa kai wani cikin annabawa na da can ne ya dawo da rai.”
20 Ya tambaye su, “Ku fa? Wa kuke cewa da ni?” Bitrus ya amsa, “Kai Almasihu ne wanda ya zo daga wurin Allah.”
21 Sai Yesu ya gargade su da karfi, kada su gayawa kowa haka tukuna.
22 Sa'annan ya ce, “Dan Mutum dole ya sha wahalar abubuwa da yawa; dattawa za su ki shi da manyan fristoci da marubuta, sa'annan za a kashe shi. Bayan kwana uku, za a tashe shi da rai.”
23 Sai ya ce da su duka, “Dukan wanda ya ke so ya biyo ni, dole ne ya yi musun kansa, ya dauki gicciyen sa kulluyomin, ya biyo ni.
24 Dukan wanda yake so ya ceci ransa, za ya rasa shi, amma dukan wanda ya ba da ransa domina, za ya cece shi.
25 Wacce riba mutum zai samu idan ya sami duniya duka, amma ya rasa ransa?
26 Dukan wanda yake jin kunya ta da magana ta, Dan Mutum ma zai ji kunyarsa, sa'adda ya dawo cikin darajarsa da darajar Uba da ta mala'iku masu tsarki.
27 Amma ina gaya maku wannan tabbas, wadansu cikinku da ke nan tsaye, ba za su mutu ba sai sun ga mulkin Allah.”
28 Kwana takwas bayan Yesu ya fadi wadannan kalmomi, sai ya dauki Bitrus da Yahaya da Yakubu, ya hau kan dutse domin ya yi addu'a a can.
29 Sa'anda ya ke yin addu'a sai yanayin fuskar sa ya canza sosai, tufafinsa kuma suka yi sheki da haske kamar walkiya.
30 Nan da nan sai ga mutane biyu suna magana da shi, wato Musa da Iliya.
31 Suka bayyana da daraja kewaye da su, suka yi magana da Yesu a kan tafiyarsa wadda za ta zo ba da dadewa ba a cikin Urushalima.
32 Bitrus da almajiran da suke tare da shi barci mai nauyi ya dauke su. Sa'adda suka farka sai su suka ga daukakar Yesu; kuma suka ga mutanen su biyu da ke tsaye tare da shi.
33 Sa'adda Musa da Iliya suke shirin su bar wurin Yesu, sai Bitrus ya ce, “Ya shugaba, ya yi kyau da muke a nan. Zai yi kyau mu yi runfuna uku, daya dominka, daya domin Musa, daya kuma domin Iliya.” Amma hakika bai san abin da ya ke fadi ba.
34 Sa'adda yake fadin haka sai wani girgije ya zo ya rufe su. Sai suka ji tsoro sa'adda girgijen ya kewaye su.
35 Sai ga wata murya daga cikin girgijen tana cewa, “Wannan Dana ne wanda na zaba, ku ji shi.”
36 Sa'adda muryar ta gama magana, Yesu yana nan shi kadai. Suka yi shiru ba su iya cewa kome ba a kan abin da suka gani a kwanakin nan.
37 Washe gari, da suka sauko daga kan dutsen, sai taron mutane da yawa suka zo wurinsa.
38 Nan da nan, wani mutum daga cikin taron mutanen ya yi magana da karfi, “Mallam, kayi wani abu dominka taimaki da na, shi kadai ne gare ni.
39 Mugun ruhu ya kan hau kansa, ya sa shi ya yi ta magowa. Ya kan girjiza shi da karfi ya sa bakinsa ya yi ta kumfa. Da kyar ya ke rabuwa da shi, kuma ya kan ji masa ciwo ba kadan ba bayan da ya bar shi.
40 Na roki almajiran ka su umurci mugun ruhun ya fita daga cikinsa, amma ba su iya ba!”
41 Yesu, ya amsa, ya ce, “Ku karkatattun tsara marasa bangaskiya, har yaushe zan zauna da ku ina jimrewa da ku? “Kawo yaronka anan.”
42 Sa'adda yaron yake zuwa, sai mugun ruhun ya fyada yaron a kasa, ya jijjiga shi sosai. Amma Yesu ya tsauta wa mugun ruhun, ya warkar da yaron. Sa'annan ya mika yaron wurin mahaifinsa.
43 Dukansu suka yi mamaki da girman ikon Allah. Amma sa'anda suke ta yin mamaki a kan dukan al'ajiban da ya yi, ya ce da almajiransa,
44 “Ku saurara da kyau a kan abin da zan gaya maku, ba da dadewa ba za a bada Dan Mutum ga mutane.”
45 Amma almajiran ba su gane abin da yake nufi da haka ba, an hana su fahimta, domin kada su gane abin da ya ke nufi tukuna, kuma suna jin tsoron su tambaye shi.
46 Wani lokaci, almajiran suka fara gardama a tsakaninsu game da wanene za ya zama mafi girma a cikinsu.
Luka 9 in Litafi Mai-tsarki