Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 7:22-44 in Hausa

Help us?

Luka 7:22-44 in Litafi Mai-tsarki

22 Yesu, ya amsa ya ce masu, “Bayan kun tafi, ku ba Yohanna rahoton abin da ku ka ji da abin da ku ka gani. Makafi suna ganin gari, guragu suna tafiya, ana kuma tsarkake kutare. Kurame suna ji, ana tayar da matattu, ana gaya wa matalauta labari mai dadi.
23 Mai albarka ne mutumin da ya tsaya a kan ba da gaskiya gare ni saboda ayukan da na ke yi.”
24 Bayan da mutanen da Yahaya ya aiko suka tafi, Yesu ya fara yi wa taron magana game da Yahaya. “Me ku ka tafi ku gani a cikin hamada, ciyawa wadda iska ta ke girgizawa?
25 Amma me ku ka tafi domin ku gani, mutum mai saye da tufafi masu taushi? Duba mutanen da su ke saye da tufafi masu daraja, kuma suna rayuwa cikin jin dadi suna fadar sarakuna.
26 Amma me ku ka tafi domin ku gani, annabi ne? I, ina gaya ma ku, ya ma fi annabi.
27 Wannan shine wanda aka rubuta a kansa, “Duba, ina aika manzo na a gabanka, wanda za ya shirya maka hanya a gabanka.
28 Ina gaya maku, a cikin wadanda mata suka haifa, ba wanda ya fi Yahaya girma. Duk da haka, wanda ya fi kankanta a mulkin Allah, ya fi shi girma.
29 Sa'anda dukan mutane suka ji haka, har da ma su karbar haraji, suka shaida Allah mai adalci ne. Su na cikin wadanda Yahaya ya yi wa baftisma.
30 Amma Farisawa da wadanda su ke kwararru a cikin shari'ar Yahudawa, wadanda ba shi ne ya yi masu baftisma ba, suka yi watsi da hikimar Allah don kansu.
31 Sa'annan Yesu ya ce, “Da me zan kamanta mutanen wannan zamani? Da me suka yi kama?
32 Suna kama da yaran da suke wasa a kasuwa, wadanda suke magana da junansu suna cewa, “Mun yi maku busa, ba ku yi rawa ba. Mun yi makoki, ba ku yi kuka ba.”
33 Haka, Yahaya ya zo, bai ci gurasa ba, bai sha ruwan inabi ba, amma ku ka ce, 'Aljani ne yake mulkinsa.
34 Dan Mutum, ya zo, yana ci, yana sha, amma, kuka ki shi, kuna cewa dubi mutum mai hadama, mai shan ruwan inabi da yawa, abokin masu karbar haraji da masu zunubi!
35 Amma hikimar Allah tana shaidar dukan 'yayanta.”
36 Wata rana wani Bafarise, ya roki Yesu ya je ya ci abinci tare da shi. Bayan da Yesu ya shiga gidan Bafarisen, ya zauna a teburi domin ya ci abinci.
37 Sai ga wata mace mai zunubi, ta fito daga cikin birni. Sa'anda ta ji labari Yesu yana gidan Bafarisen, domin ya ci abinci. Ta dauki tandun mai na alabastar mai kamshi.
38 Ta tsaya kusa da Yesu tana kuka. Ta fara jika kafafunsa da hawayenta, tana shafe kafafunsa da gashin kanta. Tana yi wa kafafunsa sumba, tana shafe su da turare.
39 Sa'anda Bafarisen da ya gaiyaci Yesu, ya ga haka, sai ya yi tunani a cikin ransa, da cewa, “In da wannan mutum annabi ne, da ya gane ko wacce irin mace ce, wannan da take taba shi, ita mai zunubi ce.”
40 Yesu ya amsa ya ce masa, “Siman, ina so in gaya maka wani abu.” Ya ce, “malam sai ka fadi!”
41 Yesu ya ce, “wani mutum mai ba da bashi yana bin wadansu mutane su biyu kudi, yana bin dayan sule dari, dayan kuma yana bin sa sule hamsin.
42 Da yake ba su da kudin da za su iya biyan sa, sai ya yafe masu, su duka biyu. A cikin su biyu, wanne ne zai fi nuna kauna ga wannan mutum?”
43 Siman ya amsa ya ce, “Ina tsammani wanda ya yafe wa kudi da yawa.” Yesu ya amsa ya ce masa, “Ka shari'anta dai dai.”
44 Yesu ya juya wajen matar, ya ce da Siman, “Ka ga matan nan. Na shiga gidanka. Ba ka ba ni ruwa domin kafafuna ba, amma ita ta ba ni, da hawayenta ta wanke kafafuna, ta kuma shafe su da gashin kanta.
Luka 7 in Litafi Mai-tsarki