17 Yesu ya ce masu, “Menene ku ke magana akai sa'adda ku ke tafiya?” Suka tsaya a wurin suna bakin ciki.
18 Daya daga cikinsu, mai suna Kiliyobas, ya amsa masa, “Kai ne kadai mutumin da ke Urushalima wanda bai san abubuwan da suka faru a can a wannan kwanakin ba?”
19 Yesu ya ce masu, “Wadanne abubuwa?” Suka amsa masa, “Abubuwa game da Yesu ba Nazarat, wanda ya ke annabi ne, mai manyan ayuka da kalmomi daga Allah da kuma mutane.
20 Da yadda manyan firistoci da masu mulkinmu suka bada shi domin a hukunta shi ga mutuwa a kuma giciye shi.
21 Amma mun yi begen cewa shine wanda za ya yantar da Isra'ila. I, bayan wannan kuma, yanzu kwana uku kenan tunda wadannan abubuwan suka faru.
22 Amma har'ila yau, wadansu mata da ke tare da mu sun yi mana abin al'ajabi, da suka kasance a kabarin tunda sassafe.
23 Sa'adda ba su sami jikinsa ba, suka zo, da cewa su ma sun ga wahayin mala'iku wadanda suka ce masu ya na da rai.
24 Wasu maza wadanda ke tare da mu suka tafi kabarin, suka tarar da shi kamar yadda matan suka fada. Amma ba su ganshi ba.”
25 Yesu ya ce masu, “Ku mutane masu wauta da marasa ba da gaskiya ga abin da annabawa suka fada!
26 Bai zama dole ne Almasihu ya sha wahalan wadannan abubuwan ba, ya kuma shiga cikin daukakarsa?”
27 Sa'annan da farko daga Musa da har zuwa dukan annabawa, Yesu ya fasara masu duka abubuwa da ke game da kansa a dukan littattafai.
28 Da suka yi kusa da kauyen, inda suke tafiya, ko da yake Yesu ya yi kamar zai wuce su.
29 Amma suka tilasta shi, cewa, “Ka zauna da mu, gama yamma ta yi kusa rana kuma ta kusa karewa.” Sai Yesu ya tafi ya zauna da su.
30 Ya faru cewa, sa'adda ya zauna tare da su domin ya ci abinci, sai ya dauki gurasan, ya albarkace shi, ya kakkarya, sai ya ba su.