Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 23:33-49 in Hausa

Help us?

Luka 23:33-49 in Litafi Mai-tsarki

33 Sa'adda suka zo wurin da a ke kira kwalluwa, nan suka giciye shi da barayin, daya daga hannun damansa dayan kuma daga hannun hagu.
34 Yesu yace, “Uba, ka yafe masu, gama basu san abin da suke yi ba.” Sai suka jefa kuri'a, suka rarraba tufafinsa.
35 Mutane sun tsaya suna kallo sa'annan masu mulki suna ta yin masa ba'a, cewa, “Ya ceci wadansu. Bari ya ceci kansa, idan shine Almasihu na Allah, zababben nan.”
36 Sojojin ma suka yi masa dariya, suna zuwa wurinsa, suna mika masa ruwan tsami,
37 suna cewa, “Idan kai Sarkin Yahudawa ne, ceci kanka.”
38 Akwai wata alama bisansa, “Wannan shine Sarkin Yahudawa.”
39 Daya daga cikin barayi wanda aka giciye, ya zage shi, cewa, “Ba kai ne Almasihu ba? Ka ceci kanka da mu.”
40 Amma dayan ya amsa, ya tsauta masa cewa, “Ba ka tsoron Allah, da yake shari'arka daya ne da nasa?
41 Mu kam an yi ma na daidai, gama mun samu bisa ga abin da muka yi. Amma wannan mutum bai yi wani abu mara kyau ba.”
42 Sai ya kara, “Yesu, ka tuna da ni sa'adda ka shiga mulkinka.”
43 Yesu ya ce masa, “Gaskiya ina ce maka, yau za ka kasance tare da ni a firdausi.”
44 Anan nan a wajen sa'a na shida, sai duhu ya mamaye kasar duka har zuwa sa'a na tara
45 sa'adda rana ya fadi. Sai labulen haikalin ya rabu a tsakiya zuwa kasa.
46 Da kuka da murya mai karfi, Yesu yace, “Uba, na mika Ruhu na a hannunka.” Bayan da ya fadi wannan, sai ya mutu.
47 Sa'adda jarumin ya ga abin da ya faru, ya daukaka Allah, cewa, “Lallai wannan mutumin mai adalci ne.”
48 Sa'adda dukan taro mai yawa wadanda suka zo tare domin su shaida da idanunsu suka ga abubuwan da suka faru, suka koma suna bugan kirjinsu.
49 Amma duk idon sani, da kuma matan da suka bi shi tun daga Galili, suka tsaya daga nesa, suna duban wadannan abubuwa.
Luka 23 in Litafi Mai-tsarki