1Anan nan idin gurasa mara yisti ya yi kusa, wanda a ke kira Idin ketarewa.
2Manyan firistoci da marubuta suka yi shawara yadda za su kashe Yesu, gama suna jin tsoron mutane.
3Shaidan ya shiga Yahuza Iskariyoti, daya daga cikin goma sha biyun.
4Yahuza ya je ya yi shawara da manyan firistoci da Jarumawa yadda zai ba da Yesu a garesu.
5Suka yi farin ciki, suka yarda su ba shi kudi.
6Sai ya yarda, sai ya nimi dama yadda zai ba da shi garesu a lokacin da babu taro.
7Ranar idin gurasa mara yisti ya yi, da dole za a yi hadayan rago na Idin ketarewa.
8Yesu ya aiki Bitrus da Yahaya, ya ce masu, “Ku je ku shirya mana abincin Idin ketarewa, domin mu ci.”
9Suka tambaye shi, “A ina ka ke so mu shirya?”
10Ya amsa masu, “Ku ji, sa'adda ku ka shiga birnin, wani mutum mai dauke da tulun ruwa zai same ku. Ku bishi zuwa cikin gidan da za ya shiga.
11Sai ku gaya wa mai gidan, 'Malam ya ce, “Ina dakin baki, inda zan ci abincin Idin ketarewa da almajirai na?'”
12Zai nuna maku babban bene wanda yake a shirye. Ku shirya a can.”
13Sai suka tafi, suka sami komai kamar yadda ya gaya masu. Sai suka shirya abincin Idin ketarewan.
14Sa'adda lokacin ya yi, ya zauna da almajiran.
15Sai ya ce masu, “Ina da marmari matuka in ci wannan abincin Idin ketarewa da ku kamin in sha wahala.
16Gama na ce maku, ba zan ci shi kuma ba, sai dai an cika shi a mulkin Allah.”
17Sai Yesu ya dauki koko, sa'adda ya yi godiya, sai yace, “Karba wannan, ku rarraba a tsakaninku.
18Gama ina ce maku, ba zan sha wannan ruwan inabi kuma ba, sai dai mulkin Allah ya zo.”
19Sai ya dauki gurasa, sa'adda ya yi godiya, ya kakkarya shi, sai ya ba su, cewa, “Wannan jikina ne wanda aka bayar dominku. Ku yi wannan domin tunawa da ni.”
20Sai ya dauki kokon kuma bayan jibi, cewa, “Wannan koko sabon alkawari ne cikin jinina, wanda aka zubar dominku.
21Amma ku yi lura. Wanda zai bashe ni yana tare da ni a teburi.
22Gama Dan Mutum zai tafi lallai kamar yadda aka kaddara. Amma kaiton wannan mutum da shine za ya bashe shi!”
23Sai suka fara tambaya a tsakaninsu, wanene a cikinmu da zai yi wannan abu.
24Sai gardama ta tashi a tsakaninsu game da wanene mafi girma.
25Ya ce masu, “Sarakunan al'ummai suna nuna iko akansu, kuma wadanda suke da iko a kansu ana ce da su masu mulki da daraja.
26Amma kada ya zama haka da ku. A maimakon haka, bari wanda ya ke mafi girma a cikinku ya zama mafi kankanta. Bari wanda yafi muhimmanci kuma ya zama kamar mai hidima.
27Gama wanene yafi girma, wanda ya zauna a teburi, ko kuwa wanda yake yin hidima? Ba wanda ya zauna a teburi ba? Duk da haka ina kamar mai hidima a tsakaninku.
28Amma ku ne wadanda ku ke tare da ni a cikin jarabobina.
29Na baku mulki, kamar yadda Ubana ya ba ni mulki,
30domin ku ci ku kuma sha a teburi na mulkina. Za ku zauna a kan kursiyai kuna shari'anta kabilun nan goma sha biyu na Israila.
31Siman, Siman, ka yi hankali, shaidan ya nemi izini a bada kai domin ya tankade ka kamar alkama.
32Amma na yi maka addu'a, saboda kada bangaskiyarka ta fadi. Bayan da ka juyo kuma, ka karfafa 'yan'uwanka.”
33Bitrus ya ce masa, “Ubangiji, ina shirye in tafi tare da kai zuwa cikin kurkuku da zuwa mutuwa.”
34Yesu ya amsa masa, “Ina gaya maka, Bitrus, kamin caran zakara a yau, za ka yi musu na sau uku cewa ba ka sanni ba.”
35Sa'annan Yesu ya ce masu, “Lokacin da na aike ku babu jaka, ko burgami ko takalma, ko kun rasa wani abu? Sai suka amsa, “Babu.”
36Ya kuma ce masu, “Amma yanzu, wanda ya ke da jaka, bari ya dauka, da kuma burgami. Wanda ba shi da takobi sai ya sayar da taguwarsa ya sayi guda.
37Gama ina ce maku, abin da aka rubuta game da ni dole sai ya cika, 'An lisafta shi kamar daya daga cikin masu karya doka.' Gama abinda aka fada akaina ya cika.”
38Sai suka ce, “Ubangiji, duba! Ga takuba biyu.” Sai ya ce masu, “Ya isa.”
39Bayan cin abincin yamma, Yesu ya tafi, kamar yadda ya saba yi, zuwa dutsen Zaitun, sai almajiran suka bi shi.
40Sa'adda suka iso, ya ce masu, “Ku yi addu'a domin kada ku shiga cikin jaraba.”
41Ya rabu da su misalin nisan jifa, sai ya durkusa kasa ya yi addu'a,
42yana cewa “Uba, in ka yarda, ka dauke wannan kokon daga gareni. Ko da yake ba nufina ba, amma bari naka nufin ya kasance.”
43Sai mala'ika daga sama ya bayyana a wurinsa, yana karfafa shi.
44Yana cikin wahala sosai, sai ya dukufa cikin addu'a, har zufarsa kuma tana diga a kasa kamar gudajen jini.
45Sa'adda ya tashi daga addu'arsa, sai ya zo wurin almajiran, ya same su suna barci domin bakin cikinsu,
46sai ya tambaye su, “Don me kuke barci? Tashi ku yi addu'a, saboda kada ku shiga cikin jaraba.”
47Sa'adda yana cikin magana, sai, ga taron jama'a suka bayana, tare da Yahuza, daya daga cikin sha biyun, ya na jagabansu. Sai ya zo kusa da Yesu domin ya yi masa sumba,
48amma Yesu ya ce masa, “Yahuza, za ka ba da Dan Mutum da sumba?”
49Sa'adda wadanda suke kewaye da Yesu suka ga abin da yake faruwa, sai suka ce, “Ubangiji, mu yi sara da takobi ne?”