Text copied!
Bibles in Hausa

Luka 17:11-25 in Hausa

Help us?

Luka 17:11-25 in Litafi Mai-tsarki

11 Wata rana yana tafiya zuwa Urushalima, sai ya bi iyakar kasar Samariya da Galili.
12 Yayin da yana shiga wani kauye kenan, sai wadansu kutare maza guda goma suka tarye shi suna tsaye daga nesa da shi
13 sai suka daga murya suka ce, “Yesu, Ubangiji, ka yi mana jinkai.”
14 Da ya gan su, ya ce masu, “Ku je ku nuna kanku a wurin firistoci.” Ya zama sa'adda suke tafiya, sai suka tsarkaka.
15 Daya daga cikinsu da ya ga an warkar da shi, ya koma, yana ta daukaka Allah da murya mai karfi.
16 Ya fadi a gaban Yesu, yana masa godiya. Shi kuwa Basamariye ne.
17 Yesu ya amsa ya ce, “Ba goma ne aka tsarkake ba? Ina sauran taran?
18 Babu wani da ya dawo ya girmama Allah sai wannan bakon kadai?”
19 Sai ya ce masa, “Tashi, kayi tafiyarka. Bangaskiyarka ta warkar da kai.”
20 Da Farisawa suka tambaye shi lokacin da mulkin Allah zai bayyana, Yesu ya amsa masu ya ce, “Mulkin Allah ba lura ake yi da shi ba.
21 Ba kuwa za a ce, 'Gashi nan!' Ko kuwa, 'Ga shi can ba!' domin mulkin Allah yana tsaknaninku.”
22 Yesu ya ce wa almajiran, “Kwanaki na zuwa da za ku yi begen ganin rana daya cikin ranakun Dan Mutum, amma ba zaku gani ba.
23 Za su ce maku, 'Duba can! 'Duba nan!' Amma kada ku je kuna dubawa, ko kuwa ku bi su.
24 Kamar yadda walkiya take haskakawa daga wannan bangaren sararin sama zuwa wancan bangaren, haka ma dan mutum zai zama a ranar bayyanuwarsa.
25 Amma lalle sai ya sha wahaloli dabam dabam tukuna, mutanen zamanin nan kuma su ki shi.
Luka 17 in Litafi Mai-tsarki